A wata tattaunawa da yayi da jaridar Daily Trust tsohon gwamnan Kaduna, kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana cewa, a duk cikin 'yan takarar PDP shine 'yan APC suka fi shakka.
Makarfi yayi wannan maganane a lokacin da yake bayar da amsar tambayar da jaridar ta mishi na cewa, ina gaskiyar rade-radin da akeyi na cewa, zai bar PDP?
Yace bazai bar PDP zuwa wata jam'iyya ba ya fada a baya kuma zai sake fadi, idan ya bar PDP to ya bar siyasa kenan dan baiga abinda zai je ya nema a wata jam'iyya ba.
Ya kuma ce ya lura a shafukan sada zumunta masu yada wannan rade-radi yawanci 'yan APC ne dalili kuwa shine suna ganinshi a matsayin wanda suka fi shakkar haduwa dashi a babban zabe saboda cikin 'yan takarar PDP kaf babu wanda zai basu mamaki kamarshi.
Post a Comment