Tun yana yaro wata larurar rashin lafiya ta sa Yahaya ya daina gani.
A hakan ya yi sana'o'i daban-daban, kama daga yin ice zuwa sai da kayan provision , kafin daga karshe ya koma bara.

sai dai kuma daga bisani ya fahimci cewa bara ba ta da amfani, sannan ya gano cewa Allah Ya yi masa baiwa ta iya sarrafa kalmomi, don haka sai ya koma waka.
Da farko dai wakokin siyasa yake yi, amma sai ya ga 'yan siyasar suna daukar mawaka a matsayin mabarata.

"Abin da ko ya sa nake irin wannan tunanin shi ne: wakar da zan yi yau a ban N50,000 saboda ba na gani, akwai mutumin da saboda yana gani ba zai yi wakar da ta kai ta kyau ba, amma za a ba shi N100,000 ko sama da haka", inji Malam Yahaya.
Saboda haka ne ma ya koma wakar fadakar da al'umma, a cewarsa, kuma bayan ya kaddamar da wani faifan wakokinsa kwanaki ya yi amfani da kudin wajen kafa wata cibiya ta horar da nakasassu da nufin yaye su daga bara.
Da yake an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi, latsa alamar lasifikar da ke sama don jin bayanin da Malam Yahaya ya yi game da wannan batu.

Sources:bbchausa.com

Post a Comment

 
Top