- An gano cewa Mallam Ibrahim Shekaru yana tattaunawa da Gwamna Ganduje kan batun sauya sheka zuwa APC

- Wata kwakwaran majiyar ta ce Shekarau ya fara tattaunawa da Osinbajo ne amma daga baya ya cigaba tattaunawar

- Majiyar ta ce Shekarau ya APC tayi alkawarin bawa Shekarau Minista amma ya ce Sanata ya ke so kuma yana son a bashi damar zabar mataimakin gwamna a Kano

Daily Nigerian ta ruwaito cewa ta samu daga kwakwaran majiya cewa tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, yana tattaunawa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo tun lokacin da 'yan siyasa suka fara rububin sauya sheka.

Majiyar ta ce jam'iyyar APC ta yiwa Malam Shekarau wasu alkawurra ciki har da kujeran Minista idan har ya amince ya bar jam'iyyar PDP ya komo APC.

Duk da an ce Osinbajo ne ya fara tattaunawar da Shekarau, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ne ya yi wannan yarjejeniyar dashi idan har zai amince ya fice daga PDP.

Wasu na kusa da Shekarau da suka hallarci tattaunawar sunce Malam Shekarau ya nemi a bashi kujerar takarar Sanata kana a bashi damar fitar da dan takarar mataimakin gwamna a jihar Kano.

Daily Nigerian ta gano cewa Mallam Shekarau yana son ya Ganduje ya amince da Umar Maimansaleta a matsayin mataimakin gwamna amma gwamna Ganduje baiyi maraba da batun ba.

"Kowa ya san cewa Shekarau na da rawar da zai iya takawa a zaben kuma muna son ya dawo APC, sai dai duk hakan, Ganduje baya son ya amince da mataimakin gwamna da zai rika yiwa wani daban biyaya.

"Ganduje baya son maimaita abin da ya faru da Farfesa Hafizu, haka yasa yake son ya zabi wani daban da jama'a ke so daga cikin na kusa dashi," a cewar majiyar da ta nemi a sakayya sunanta.

Har ila yau, majiyar ta ce, Ganduje na iya amincewa zai yi takara da Maimansaleta a matsayin mataimakinsa amma ya zagaya majalisar jihar Kano ya nemi su ki amincewa da shi
Read more at: https://ift.tt/2wMX8h0

Post a Comment

 
Top