Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya tabbatar da cewa idan aka sake zabar gwamnatin shugaba Buhari zata tabbatar da samar da wutar lantarki na tsawon awanni 24.


Amaechi ya bayar da wananan tabbaci ne a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja, jiya Talata, kamar yanda jaridar Daily post ta ruwaito.

Ya kuma yi magana akan jami'ar sufuri da za'a gina a mahaifar shugaban kasa, Daura,jihar Katsina, yace babu wani abin cece kuce akan kai jami'ar Daura saboda Daura ma ai Najeriyace.

Inda sunso sai su kaita Fatakwal ko Sakkwato ko Enugu, dan haka kaita Daura ba wani matsala bane. Ya kara da cewa, shugaban kasa baima da labarin cewa shi Amaechin zai zabi kai jami'ar Daura.

Ya kara da cewa, maganar wutar lantarki kuwa suna samun megawat dubu 3000 zuwa dubu 7000 yace amma 5000 kawai suke samun rarrabawa saboda kayan aikin na da matsala amma ana nan ana kan gyaransu kuma idan aka basu dama samun wutar zai iya kaiwa 24.

Post a Comment

 
Top