A tattaunawa ta musamman da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya ke yi da fitaccen malamin addinin Islama kuma dan siyasa a jihar Kano, MALAM IBRAHIM KHALIL, mako-mako a wannan satin mun dora daga inda mu ka tsaya, inda malamin fara bayani kan batun jam’iyyu, sannan ya gangara kan Izala da darika, sai kuma kan ya tsaya kan batun tsayar da tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, a zaben 2003.
Ga yadda tattaunawar cigaba: Tun da ka shiga siyasa a layi daya ka ke na APP zuwa ANPP zuwa APC. Shin me ya sa ba ka taba tsallaka wa ka shiga PDP ba duk cewa a baya ta na ikirarin ita ce jam’iyya mafi girma a Afrika? Babban abinda mu ke so mu gina tunanin mutane a kai shi ne manufa. Dalilin da zai sa na bar layin APC babu shi. Dalilin da zai sa dan PDP ya bar ta ya dawo APC shi ya san shi.
Haka ma dalilin da zai sa dan APC ya bar ta ya koma PDP shi ya sani. Amma ni tsarina babu wannan, amma ban ce ba zai yiwu ba. Misali; idan a ka wayi gari a ka ce akwai dan takara mai zaman kansa (Independent), ai ka ga mu can za mu tafi, saboda zai fi sauki zuwa ga gina kasa, gina al’umma da gina tunani mai kyau fiye da ka na nan ko ka na can (jam’iyya), saboda duk lokacin da jam’iyyu su ka samu canjin shugabanci su kan canza salo ko su canja tsari ko su canja manufa da tafiya, amma idan a ka ce akwai dan takara mai zaman kansa, to ka ga wannan salon zai samu canji ne daga dai-daikun mutane, amma ba zai canja kasa gabadaya ba.
To, da ka yi maganar zaman kai (Independent) ko da a wajen sha’anin karantarwa a na kallon ka a matsayin indifenda, wato ba ka yin Izala ba ka yin darika, kamar ka na tsakiya. Shin me za ka ce kan hakan? A’a, ni ba a tsakiya na ke ba. Ni Musulmi ne sak! Ai idan ka ji mutum ya na tsakiya, wato kamar mutum ya na kan katanga kenan. Ai da ma duk Musulman ne, amma kai ba ka Izala ba ka darika a ke nufi.
A’a, ni Musulmi ne sak! Sunana kenan, Musulmi har abada, kuma a lokaci guda na yarda dan darika Musulmi, dan Izala Musulmi ne, kuma kowannensu ya na da abubuwa da yawa na alheri kuma ba zai rasa wani abu na kuskure ba, kamar yadda ni ma ba zan rasa wani abu na kuskure ba. Na yarda mu ’yan indifenda ne, amma a lokaci guda mu na girmama dan Izala mu na girmama dan darika, domin kowannensu Allah ya ke nufi, Allah ya ke son ya farantawa, annabi ya ke bi, addinin Allah ya ke so kuma kowannansu so ya ke yi ya taimaka wa addinin Allah ya cigaba. Kuskuren fahimta a junansu ko rashin gane fahimtar junansu, wannan da ne, amma yanzu duk sun soma gane fahimtar junansu su ma sun fara ganewa sun daina rigima a junansu.
Amma hawa katanga da ka yi ba ka jin zai sa ’yan Izala su ga kamar ba ka damu sunnah ba? A’a, ni ban hau katanga ba, domin ni Musulmi ne. Abinda Allah da annabi ya yarda da shi, tsarin da Musulunci ya zo da shi, shi na ke yi. Ban saya wa kaina na dauki wani bangaranci ba, saboda duk wadannan bangarorin nawa ne. Ina mu’amula da su kuma Ina son su, su na da kima a idona, kuma idan na tashi yin addu’a ba na ware waninsu; dukkansu na ke yiwa. Don haka ni ba katanga na hau ba. Idan ka ga mutum ya hau katanga, ai nau’i ne na munafunci, ni kuwa kowa ya san ra’ayina, ya san tunanina, ya san fahimtata. Ban taba boye ra’ayina da fahimtata ba a ko’ina
. Ka ga don haka ba a kan katanga na ke ba; a indifenda na ke cewa ni Musulmi ne sak kuma kowane mutum ya na mu’amula da ni ne a matsayina na Musulmi, ni ma kuma Ina mu’amula da kowane mutum ne a matsayinsa na Musulmi; fahimtarsa da ta raba shi da wani, fahimta ce ta son alheri. Dan darika burinsa shi ne ya gina addini, ya tabbatar da addini, ya ja mutane zuwa ga addini. Dan Izala ma burinsa shi ne ya gina addini, ya tabbatar da addini, ya ja mutane zuwa ga addini. Sabanin da ke tsakaninsu a da, a yanzu babu mafi yawansa. Kusan ma ya zama sai dan abinda ba ka rasa ba. Amma ni ba a kan katanga na ke ba. Yanzu a misali a matsayinka na dan jarida ka je ka yi yawo ka ce, duk wanda ka hadu da shi ka ce za ka yi bincike na kidaya a kan dan Izala da dan darika, sai ka ga dan indifenda ya fi yawa. Wato bangarenku kenan?
Eh, bangarenmu ya fi yawa, domin idan ka gama ware dan darika waje daya, ka ware dan Izala waje guda, to duk sauran ’yan inidfenda ne. To, game da fatawa mai sauki da ka ke bayarwa, wasu su kan soke ka a kanta, wasu kuma su kan yabe ka a kanta. Shin wadanne ne sa ka fi tasiri a zuciyarka? Ai ni da ka soke ni, da ka yabe ni, babu daya da ya ke da wani muhalli a wurina. Saboda me? Saboda sukar nan da ka yi, ka soke ni ne don a fahimtarka ban yi daidai ba. Fahmtarka ce. Wannan yabon da ka yi min, ka yabe ni ne saboda a fahimtarka na yi daidai. Fahimtarka ce.
Ni kuma abinda kawai na ke so na tabbatar shi ne ya ya za a yi na karantar da mutane yadda za su bauta wa Allah cikin farin ciki fa jin dadi da kwanciyar hankali ba tare da sun kosa ba. Yanzu misali, mutum ya shekara 10 ba ya sallah, sai ran nan ya zo ya ce shi ya tuba zai yi sallah, na ce ya je ya rama sallar shekara 10 har kila ma ya ga ya za a yi ya iya rama har kila ma ya karaya ko kuwa na ce da shi ya roki Allah gafara ya cigaba da sallah daga yanzu tunda ba wani nassi ne na Kur’ani ya ce sai ya zo ya rama sallar ta shekara? Ka ga tuban sai ya fi ma sa kwanciyar hankali. Kamar misali mutumin da ya ranci bashin banki ne kudin ruwa su na ta hawa har sun ninka uwar kudi, sai a ka ce ya biya uwar kudin kawai sai ya roki a yafe ma sa kudin ruwan. Ka ga ya fi ma sa sauki. Idan ba haka ba karshenta gudu zai yi. Allah mai gafara ne mai jin kai ne, gara ka ba shi dama ya bauta wa Allah cikin kwanciyar hankali a kan ka zo ka tilasta shi ya rama sallar shekara 10.
Idan mu ka koma batun siyasa, a zaben 2003 a na ganin cewa ku malamai kun tsayar da Malam Ibrahim Shekarau har ya ci zaben kujerar gwamna a Kano. Shin me ya sa ba ku dauko tsantsar malamin addini ba, sai ku ka dauko dan boko? To, wannan haka kowa ya ke fada, amma ba haka abin ya ke ba.
Amma lokaci bai na a fadi yadda gaskiyar al’amura su ke ba. Don haka sai ka bar shi a haka yadda a ke fada ba wai don haka ba ne, amma sai don shi ne abinda mutane su ke fada cewa wannan dan takarar malamai ne, malamai ne su ka dauko shi. A bar shi a hakan. Kamar misali NEPU ce da a ke cewa ranar takwas ga watan takwas mutum takwas sun kafa NEPU, alhali an gama shirin kafa NEPU amma an taho a ranar da za a zo a kaddamar da ita wasu ruwa ruwa ne ya hana su zuwa, wasu kuma sun ce wasu dalilai ne su ka hana su zuwa, sai wadannan mutum takwas din ne kawai su ka samu dama su ka zo.
To, ka ga shikenan sai a ke ta cewa takwas-takwas kawai, saboda ya fi dadin fada, amma ba don su kadai su ka kafa NEPU ba. Za mu dakata a nan sai kuma makon gobe da yardar Allah.
Madafa: LadershipAyau
👉Ku aje mana ra'ayinku, yanada matukar amfani.
Post a Comment