Suna: Matar Mamman
Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo
Kamfani: Asnanic Mobie Tone
Shiryawa: Usman Mu’azu
Umarni: Aminu Saira
Jarumai: Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Hafsat Idris, Asiya Barde, da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din me kallo ya ga Uwale (Asiya Barde) ta na bacci wanda a cikin barcin ta tayi mafarkin wata gawa wadda jama’a suka dauke ta suka kai ta makabarta, bayan Uwale ta farka daga bacci a firgice sai mijinta Magaji (Isa A. Isa) yake tuhumar ta akan don me zata dinga mugun mafarki don kawai yace zai karo mata kishiya? Daga baya Magaji ya soma kokarin kwantar was da Uwale hankali a bisa dalilin sa na son kara aure amma bata saurare sa ba saboda mafarkin da tayi na gawar wata mace shi yafi tsaya mata a zuciya, hakan yasa ta tafi wajen malami ta fada masa mafarkin da tayi gami da son sanin fassarar mafarkin ta, amma sai malamin ya nuna mata cewar bazai fassara mata mafarkin ba har sai taje ta nemo bayani akan gawar matar da ta gani a mafarkin tunda ta nuna alamun cewar tasan wani makusancin gawar da ta gani. Haka kuwa Uwale ta tafi wajen Asiya (Hafsat Idris) don son sanin wacece matar da taga gawar ta a mafarki? A nan Asiya ta fara bawa Uwale labarin Mariya wadda itace Uwale ta gani a mafarkin ta, kuma Mariya (Hadiza Gabon)kawar Asiya ce wadda suka taso tare domin Asiya ce tayi mata siyan baki a lokacin auren Mariyar da mijinta Mamman (Ali Nuhu) bayan auren Mariya da Mamman sai Asiya ta cigaba da zuwa gidan Mariya a duk sanda take da lokacin hakan, kuma akwai mutunta juna a tsakanin Asiya da Mamman saboda akwai lokutan da idan tazo gidan Mariya yakan bukaci Asiya da cewar ta jira shi ya dawo daga aiki don ya sauke ta a gidan iyayen ta, akwai lokacin da Mamman ya dauko Asiya a motar sa don mayar da ita gida sai yake tambayar ta shin bata da masu son auren ta ne? Sai Asiya ta nuna masa cewar har a sannan bata samu wanda suka daidai ta ba shi yasa ma ta koma makaranta don cigaba da karatu, jin hakan ne ya bawa Mamman dama bayan ya koma gida sai ya fara turo mata sakonnin soyayya a shafin zumunta na ‘Whats’App’ bayan Asiya taga an turo mata sakonnin kulawa a wayar ta kuma da lambar da bata sani ba sai tayi mamaki gami da son sanin wanda ya turo mata sakon na kalaman soyayya, amma a cikin hirar sai Mamman ya nuna mata cewar zasu hadu da ita don ta gane wanda yake son ta, hakan kuwa akayi Asiya tana makarantar su sai taga Mamman yazo wajen ta a lokacin da tayi zaton ganin wanda yake turo mata kalaman soyayya, hakan yasa ta kasa yarda da cewar shine me turo mata sakonnin soyayya a waya sai ta fara zaton ko abokin Mamman din ne yake son ta, amma a nan take a wajen sai Mamman ya nuna mata cewar shi yake turo mata sako kuma yana son ta da aure, hakan ya bawa Asiya mamaki saboda ganin cewa ita kawar matar sa Mariya ce. Don haka sai Asiya ra roki Mamman akan ya canja shawara don bazai samu abinda yake nema a wajen ta ba.

 Da daddare kuwa Mamman ya shirya cikin kaya masu kyau ya fesa turare zai fita, amma da Mariya taga yayi wannan shirin sai ta tambaye sa inda zai je amma sai Mamman ya nuna wajen mahaifin sa zai je, jin hakan sai bai gamsar da Mariya ba sai ta fara zargin ko ya shirya yi mata kanwa ne saboda tun kafin ya aure ta yasha fada mata cewar bashi da ra’ayin zama da mace daya, amma sai Mamman ya nuna mata sam ba haka bane shi ziyara zai je. Bayan Mamman yaje wajen Asiya sai ta fito ta gargade sa akan kada ta sake ganin yazo gidan iyayen ta saboda bazata iya auren sa ba domin tana ganin yin hakan kamar zataci amanar kawar ta Mariya ne. Bayan Mamman ya koma gida sai ya cigaba da kiran wayar Asiya yana yi mata magiya akan ta so shi amma sai ta nuna sam bata amince ba. Cikin dare Mamman yana bacci sai Mariya taji shigowar sako a wayar sa, bayan ta duba ne sai ta fahimci cewa yana son ya auri kawarta Asiya, bayan ta fuskanci hakan ne sai ta soma bijiro masa da maganar tana so ya kara aure, amma sai Mamman ya nuna sam shi baya ra’ayin hakan. Asiya kuwa sai ta daina zuwa gidan Mariya sai bayan an dau tsawon wani lokaci sannan tazo, hakan ya kara saka Mariya zargi akan cewar tabbas akwai alakar dake tsakanin ita Asiya da Mamman, hakan yasa Mariya ta roki Mamman akan tana so ya auri Asiya, amma sai yayi fushi ya nuna cewar tana zargin sa da kawar ta ne, Asiya da Maryam suna cin abinci sai Mariya taji Asiya tana yabon halayen Mamman gami da nuna bai kamata ta dinga samun sa6ani dashi ba, hakan yasa Mariya ta yi amfani da wannan damar wajen bijirowa Asiya da batun tana so ta auri mijinta Mamman, amma sai Asiya taki amincewa da hakan har ma ta soma fushi da Mariya ta daina zuwa gidan, hakan yasa Mariya taje gidan iyayen Asiya ta cigaba da rokon ta akan ta auri mijinta Mamman, amma Asiya duk da hakan bata amince ba, sai dai kuma abin ya dame ta don ta rasa yadda zatayi, musamman da taga Mariya tana bibiyar ta a ko ina har a cikin makaranta don ta auri mijinta Mamman. Mariya ta yi nasarar shawo kan Mamman ya amince zai auri Asiya saboda dama can yana son ta kuma akwai lokacin da wani abokin sa ya taba bashi shawara akan tunda matar sa Mariya ta amince masa da ya karo auren wadda yake so ya dace ya amince, amma a sannan din ma dai Mamman yana nunawa abokin nasa cewar yasan kawaici ne matar sa take masa domin tana son duk abin da yake so koda kuwa ita bata son abin. Bayan Mamman ya amice da bukatar Mariya ta son ya auri kawarta amma sai ya nuna ai ba lallai Asiya ta amince da auren ba, nan ma dai Mariya ta nuna kada ya damu zata shawo kan matsalar. Haka kuwa aka yi, Mariya ta matsawa Asiya akan lallai tana so ta auri mijinta Mamman domin ko bai aure ta ba zai auro wata macen tunda yana da ra’ayin zama da mata biyu, hujjojin da Mariya ta dinga kawowa Asiya ne yasa har Asiya ta amince zata auri Mamman. Cikin dan lokaci kadan aka fara shirye shiryen aure har ma dangin Mamman suna mamakin halayyar Mariya saboda ganin da ita ake ta shagulgulan bikin auren mijinta da Asiya, a wannan lokacin ne kannen Mariya suka rutsa Asiya a makaranta suka ci mata mutunci har da marin ta saboda zata auri mijin yayar su Mariya. Wannan dalilin ne yasa mahaifiyar Asiya da kuma ita Asiyar suka janye maganar hada auren Mamman da Asiya, amma sai Mariya ta kai karar kannen nata wajen iyayen su wanda kuma su ma iyayen basu goyi bayan abinda yaran suka yi ba, har ma mahaifin su Mariya ya nuna bazai yafewa kannen Mariyar ba har sai sun je sun roki gafarar Asiya, haka kuwa aka yi sai da suka nemi yafiyar Asiya kuma Mariya ta sa baki har abin ya wuce kuma Asiya ta amince da zata auri Mamman.


Bayan auren Asiya da Mamman Mariya ce ta karbi kudin siyan baki a wajen mijin su Mamman sannan ta yi musu nasiha gaba daya na zama lafiya. Bayan gama hakan ne ta shiga daki tana kuka saboda kishin mijinta da ya dame ta amma son abinda yake so ne da bin umarnin Allah hakan ya hana ta bayyana kishin ta a sarari. Ba’a jima da yin auren Asiya da Mamman ba sai abubuwa suka soma dagule masa, ya fara yin asara, kayan sa da aka turo daga wani garin ma’aikata suka rike, ba shi ya fara hawa kan sa. Nan fa dangin Mamman suka fara kananan maganganu akan ya auro mace me kashin tsiya ga komai nasa ya fara karewa, jin hakan bai sa Mamman ya gamsu da cewar matsalar daga wajen matar sa bane, haka itama Mariya ta kara nuna masa muhimmancin yarda da kaddara. Ana cikin wannan matsalar ne Asiya ta samu juna biyu wanda hakan yasa duk sukayi ta farin ciki, musamman Mariya tafi kowa farin ciki saboda tana ganin Asiya zata haifawa Mamman dan da ita bata haifa masa ba, Asiya tana mamakin saukin kai irin na Mariya gami da rashin nuna kishi akan juna biyun da ita Asiyar ta samu, ana cikin murnar ne aka gane cewa itama Mariya tana dauke da juna biyu, nan fa murnar su ta karu saboda suna ganin sun samu abinda kudi bazai basu ba, wato haihuwa. Bayan dan wani lokaci Mariya da Asiya su ka haifi ‘ya’ya mata wadanda duk aka saka musu sunan Mariya.

Lokacin da Asiya fa gama bawa Uwale labarin Matar Mamman wato Mariya, sai Uwale taji tana nadamar abinda take shirin yi na hana mijin ta kara aure, hakan yasa bayan ta koma gida ta roki gafarar mijinta gami da nuna cewar ta amince ya kara aure, amma sai mijinta ya nuna dama zai kara aure ne saboda munanan halayen ta, amma yanzu ya fuskanci tayi nadamar sa zata iya gyara halin ta don haka shima ya fasa kara wani auren.

Abubuwan Birgewa:

1- Marubucin yayi kokari matuka wajen gina labarin, domin labarin fim din ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba.

2- (Matar Mamman) Sunan fim din ya dace sosai da labarin.

3- Labarin ya fadakar domin yana dauke da mafita kan hujjoji masu karfi wadanda suke damun al’ummar mu, musamman ma ga mata.

3- Fim din ya rike me kallo wajen son ganin abinda zai faru a gaba, sannan kuma fim din ya ta6a zuciyar me kallo kuma mutum zai ga kamar rayuwar zahiri ta wadansu mutanen yake kallo.

4- Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin, haka kuma me daukar Camera tayi kokari ta hanyar nuna salon daukar hoto me kyau. Daga hoto har sauti sun fita radau.

5- Kalaman jaruman wato (Dialogue) sun yi dadi gami da gamsar wa.

6- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin. Wato (Location)

7- Jaruman sun yi kokari matuka wajen samar da yanayin da ya dace.

Kurakurai:

1- Shin wace alaka ce a tsakanin Asiya da Uwale? Me kallo yaga Uwale taje wajen Asiya an bata labarin Matar Mamman, amma ba’a nuna dangantakar dake tsakanin Asiya da Uwalen ba. Tunda ba’a nuna Uwale a cikin jerin kawayen Asiya ba, ya dace ayi bayanin alakar su ko da ta hanyar ‘yan uwan taka ne.

2- Shin wanene mahaifin Asiya ne? Har fim din ya kare me kallo bai ji ko a baki an ambaci mahaifin ta ba, musamman a sanda maganar auren ta da Mamman ta taso da kuma sanda aka ce an fasa auren, ya dace aji an ambaci ko wani Kawun ta ne, idan ma rasuwa mahaifin nata yayi, ya kamata ko a baki ne a fada.

3- Abin daukar sauti ya leko a lokacin da Mariya da Asiya ke cin abinci a falo, sa’in da Mariya ta fara bijirowa da Mamman batun ya auri Asiya a sanda yayi fushi ya fice daga gidan.

4- An samu discontinuity a lokacin da Mamman ya shirya a karon farko da daddare don soma zuwa hira wajen Asiya, an nuna bakar doguwar riga a jikin Mariya a sanda ta shigo daki take tambayar sa inda zai je, amma bayan ya dawo sai aka ganta sanye da koriyar doguwar rigar atamfa a falo, bayan kuma tabi Mamman cikin daki sai aka sake ganin ta da bakar doguwar rigar farko.

5- Lokacin da yayar Mamman wato Yaya Fati da kanwar ta suka zo gidan Mamman bayan sun dawo daga wajen kai kayan lefe, me kallo yaji sanda Yaya Fati take cewa, tana mamakin ganin yadda Mariya ta zage dantse wajen kai kayan lefe gidan su kishiyar ta. Amma a karshen hirar sai akaji kanwar Mamman tana tambayar cewa yaushe za’a kai kayan lefen? A cikin hirar gaba daya me kallo ya fahimci an kai kayan lefen saboda ko nuna su ma ba’a yi ba, don haka bai dace a karshen hirar a ji kanwar Mamman ta tambayi shin yaushe za’a kai kayan lefen ba.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma yayi ma’ana sosai gami da gamsar da mai kallo, labarin yazo da kyakkyawan salon da zai iya yin tasiri wajen dakile mugun kishi ko mummunan zato daga wajen mata da sauran jama’a. Wallahu a’alamu!

Sources:leadershipayau

Post a Comment

 
Top