Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Jaridar Katsinapost ta fitar da rahoton cewa wasu da ake zargin 'yan-daba ne sun yi kutse cikin ofishin kamfen din Atiku Abubakar da ke kan titin Dandagoro, karamar hukumar Batagarawa, jihar Katsina, inda suka lalata ababan hawan miliyoyin naira da aka aje a farfajiyar ofishin. 

An samu rahoton cewa 'yan daban sun kai wa magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar da suka tarar a cikin ofishin farmaki. 

Kakakin tawagar kamfen din Atikun na yankin Arewa maso yammacin kasar nan, Jacob Dickson, ya ce kayayyaki na daruruwan miliyoyin naira sun salwanta yayin farmakin.

Wani ganau ba jiyau ba ya ce 'yan-daban sun fara zuwa a cikin baburan Napep guda uku domin leken asiri a kan magoya bayan jam'iyar PDPn kafin daga bisani su dawo domin kai farmakin.

"Mu (magoya bayan Atiku) mun je babban taron PDP na yankin Arewa maso yamma da aka gabatar a sakateriyar jam'iyar ta jihar Katsina sannan muka dawo ofishin kanfen dinmu wanda aka gyara domin goyon bayan takarar Atiku a babban zaben 2019. A lokacin 'yan ta'addan dauke da makami suka kawo mana farmaki," inji ganau din.

"Da fari sun zo domin leken asirinmu kafin su koma su dauko makamansu domin kaddamar da harin.

"Sun faffasa gilasai, madubai da jikin ababan hawan da aka aje a farfajiyar ofishin kamfen din da adduna, sanduna da sauran abubuwan da suke ruke da su a hannayensu. 

"Sun rushe mana katanga, sun sauke tutocin jam'iyar da suka kewaye katangar sannan kuma sun gudu da wasu tutocin jam'iyar. 

"Mun kai rahoto ofishin 'yan sandan Batagarawa sannan DPO din ofishin tare da tawagarsa sun fara bincike a kai."

Post a Comment

 
Top