Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Liberpool John W Henry ya saka kungiyar a kasuwa amma batare da duniya ta sani ba domin siyar da ita. Henry dai ya siyi Liberpool ne a shekara ta 2010 akan kudi dam milyan 343 sai dai kamar yadda wata jarida a kasar Amurka ta wallafa tace shahararren attajirin dan kasar Amurka ya saka kungiyar a kasuwa.

An bayyana cewa Henry, wanda a halin yanzu shine mamallakin kamfanonin MLB outfit Boston Red Sod, yana bukatar fam biliyan daya da miliyan 54 ga duk wanda yake son ya siyi kungiyar mai tarihi a kasar Ingila. Liberpool dai tayi rashin nasara daci 2-0 a wasan cin kofin zakarun turai data buga da kungiyar Red Star Belgrade a ranar Talata sai dai akwo yanzu babu kungiyar data samu nasara akanta a gasar firimiyar kasar Ingila. Kungiyar itace a matsaki na uku akan teburin gasar da maki 27 bayan buga wasan sati na sha daya kuma a wanann satin zata buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Brighton. 

A kwanakin baya dai an bayyana cewa mamallakin kungiyar yayi fatali da tayin kusan fam biliyan biyu domin ya siyar da kungiyar bayan da akayi zargin wani dan uwan mamallakin Manchester City ne yaso ya siyi kungiyar.

Rahoto:leadershipayau.com

Post a Comment

 
Top