Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta mayar da martani akan gayyatar da shugaban kasa da amatarshi ke yiwa 'yan fim inda tace duk da abinda Buharin yawa 'yan fim amma ba su yi zuciyaba sai binshi suke.

Ummi ta kara da cewa wannan magana tana yin tane a matsayin 'yar fim ba wai 'yar siyasa ba kuma duk da yake ta bar fim amma wata rana zata iya dawowa a matsayin me shiryawa, tace Buhari ya gayyaci 'yan fim haka ma matarshi ta gayya ce su inda suka kaddamar da wakar sakamakon canji, ta ce kodai sakamakon wahala?
Ta caccaki 'yan fim din inda tace duk da karantar da Buhari ya musu na basu gurin gina Film Village amma daga baya ya kwace amma sunje suna shish shige mishi ta kara da cewa su sani fa ba wai soyayya ce tasa Buharin da matarshi ke kiransu ba, saboda mabiyan da suke da sune kuma da zarar sun ci zabe zasu watsar da su.

Gadai cikakken bayanin nata:

""SAKAMAKON CHANJI KO SAKAMAKON WAHALA"da kasa take ciki? dear my kannywood family,da farko ina taya murna ga actors maza da suka samu daman zuwa yin dinner kwanaki tare da Mr president (ogah buhari).suma daga ban garen mata actresses ina tayasu murna da suka samu daman yin launching na "SAKAMAKON CHANJI" tare da 1st lady(anty aisha) to ina da QALUBALE na zuwa wannan mayan taro da kuka halarta ku yan film din dukkanku daga mazan har matan.ba ina qalubalantar ku bane saboda ni yar PDP ce,sai dan ina qalubalantar ku a matsayina na yar film yar uwarku duk da na dena film ammah denawa danayi ba yana nufin ni ba yar film bace,film is still my profession domin zan dawo film industry sooner or later as a producer inshaa allah.dan haka qalubalantarku da nakeyi na zuwa wajen Mr president da 1st lady dinsa shine:a shekaran 2015 da ogah buhari ya zama president ya bawa kannywood industry kyautan filin shirya finafinai Wanda da turanci ake kira da (film village) daga baya kuma ya sake kwace filin yayi halin qaranta.ammah sai gashi ,to my greatest surprise ku yan film din duk da abunda ya muku na kwace film village bai dame kuba kun sake zuwa kuna shish shige musu dan neman suna.to yana da kyau kusan hakkinku da yancinku na yan kasa kusani cewar film village da kukayi requesting a Baku ai hakkinku ne domin ku talakawansa ne kuma ya zama dole shugaba yayi wa talakansa duk wani abu na cigabansa domin sai da talaka shugaba yake zama shugaba.kuma ku sani yanzu dashi mr president din da ita 1st lady din da suke Jan ku ajiki yanzu suna hada taro suna kiranku to ku sani ba so bane kamfen kawai sukeyi domin sunsan yan fim suna da masoya shiyasa suke janku a jiki yanzu dan su samu kuri'unku Dana masoyanku dan suyi tazarce a zabe mai zuwa .in abun nasu gaskiya ne meyasa da basu nemeku sun hada muku taro na karamci ba sai yanzu ?inda wata kasarce daya bada film village ya sake kwacewa to wallahi da baza su sake sauraronsa ba ammah daya ke an maida talakan nigeria wawa sai dai ayi ta amfani dashi ana ajiyewa.dan haka ku sake nazari my fellow artists.in da mai maganah yafito yayi comment kada yaji tsoro dan nima rashin tsoron ne yasa nayi maganah dan kannywood ta samu yanci !"

Post a Comment

 
Top