Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Jaridar Daily Nigerian ta fitar da rahoton cewa a yanzu haka gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana kitsa yadda za a tumbuke kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Rurum, tare da wasu manyan jami'an majalisar guda shida sakamakon binciken da ake gabatarwa a kan faya-fayen bidiyon da ke nuna gwamnan yana karbar cin hanci.

Wata majiya mai tushe ta gaya wa DAILY NIGERIAN cewar gwamnan ya shiga wata tattaunawa ta sirri da misalin karfe 1:30 na dare, 'yan lokuta kadan bayan dawowarsa Kano daga birnin Habuja. 

Majiyar ta ce gwamnan zai tsira daga tsigewa ne kawai bayan an hambarar da kakakin majalisar dokokin da sauran manyan jami'an majalisar guda shida daga mukamansu.

“Gwamnan ya hadu da wasu daga cikin mashawartansa na kusa, ciki har da mataimakin gwamna, Nasiru Gawuna; kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo da kuma shugaban jam'iyar APC, Abdullahi Abbas, inda suka yanke shawarar kitsa yadda za a tsige kakakin da sauran manyan jami'an majalisar.

“Shirin da aka tsara na karshe shi ne a yi bibiyar tushen siyasar kowanne dan majalisa, sannan sai a lallabi iyayen gidansu kan su tursasa su a kan su sanya hannu a gurin tunbuke kakakin majalisar.

A daren jiya ne Murtala Sure Garo ya tuntubi dan majalisar da ke wakiltar Kunci da Tsanyawa, Garba Ya'u Gwarmai, kan ya zamo mutumin da zai hada su da tsohon kakakin majalisa, Abdullahi Ata domin ya harhado kawunan sauran 'yan majalisar da ke bangarensa.

“Za a sanya dukkan dan majalisar da ya amince kan zai aikata hakan yai rantsuwa sannan a biya shi."

Post a Comment

 
Top