Tambaya


  Assalamu alaikum Malam menene ingancin hadisin da yake cewa: "Annabi SAW ya hana kashe Kwadi saboda kukansu Tasbihi ne ga Allah"? 


 Amsa 

 Wa alaikum assalam, Tabbas ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lambata: (5269) da kuma Nas'i (2/202) cewa: wani likita ya tambayi Manzon Allah akan kashe kwadi saboda sanyawa a magani sai Annabi ya hana shi kashe su".  Baihaki ya rawaito daga maganar Abdullahi Bn Amri bn Al-Ass cewa "Kada Ku kashe kwadi saboda kukansu tasbihi ne ga Ubangijinsu". Duk da cewa hadisin zai iya daukar cewa ya ji ne daga Manzon Allah saidai Hafiz Bn Hajar yana cewa " Abdullahi bn Amr bn Ass ya shahara da yin riwaya daga malaman Yahudu da Nasara don haka ba dole ne ya zama daga Annabi SAW ya ji ba.  Kashe kwadi haramun ne saboda hadisin Abu-dawud da Nasa'i da ya gabata, kamar yadda cin su ma haramun ne, saboda ba zai yiwu a ci dabba ba sai bayan ranta ya fita.  Allah ne mafi sani  

 Amsawa
✍🏻  DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 11/11/2018

®Darulfatawa.com

Post a Comment

 
Top