Kungiyar gwamnonin Nigeria NGF za su sake tura wata tawaga don ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karin mafi karancin albashi zuwa N30,000


A baya dai gwamnonin sun cimma matsaya kan kara mafi karancin albashin zuwa N22,500 sai dai a mamakinsu, sun gano cewa kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa don cimma matsaya kan karin mafi karancin albashi bai ko kula da wannan bukatar tasu ba, da sunan cewa lokaci ya kure.

Taron kungiyar gwamnonin na daren ranar Laraba wanda ya gudana karkashin shugaban kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, ya cimma matsaya "kan cewar za a sake canje canje da kuma tura wani kwamiti don ganawa da shugaban kasa, tare da sanar da shi bukatar warware matsalolin da ke tattare da biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi, sai ko idan kungiyar kwadago za ta amince da rage ma'aikata a kasar ko kuma ita gwamnatin tarayya ta kara yawan kasafin kudin da take aikawa kowacce jiha."

Kwamitin da kungiyar ta kafa don ganawa da shugaban kasa Buhari sun hada da gwamnonin jihohin Legas, Kebbi, Filato, Bauchi, Akwa Ibom, Ebonyi da kuma Enugu.

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kwamitin da ya kafa don cimma matsaya kan karin mafi karancin albashin, wanda tun a lokacin ya sha alwashin tura umurni na sabuwar doka ga majalisun tarayyar kasar kan sabon karin mafi karancin albashin.


A cewar kungiyar gwamnonin, hanya daya ce kawai jihohi za su iya kara mafi karancin albashi zuwa N30,000, ita ce rage yawan ma'aikata ko kuma ta kara kasafin kudin jihohi

- Kwamitin da kungiyar ta kafa don ganawa da shugaban kasa Buhari sun hada da gwamnonin jihohin Legas, Kebbi, Filato, Bauchi, Akwa Ibom, Ebonyi da kuma Enugu

A wani taron gagawa da kungiyar gwamnonin Nigeria NGF suka gudanar a daren ranar Laraba a Abuja, an cinma matsaya kan sake tura wata tawaga don ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari don bayyana masa matsayar gwamnonin kan karin mafi karancin albashi zuwa N30,000.

Gwamnonin sun jaddada cewa duk da cewa suna a shirye don biyan ko nawa ne aka kayyade, kamar yadda kungiyoyin kwadago ke son kowacce jihar ta rinka biyan N30,000, to kuwa za a talauta jihohin cikin kankanin lokaci.

A cewar kungiyar gwamnonin, hanya daya ce kawai jihohi za su iya kara mafi karancin albashi har zuwa N30,000, ita cerage yawan ma'aikatan da kowacce jiha ke da su, ko kuma ita gwamnatin tarayya ta kara kasafin kudin da take turawa jihohin a kowanne wata.

Sources:legithausa.ng

Post a Comment

 
Top