Bayan nasarar da Najeriya ta samu na zuwa gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika, tauraron dan kwallon
Najeriya,Ahmed Musa ya saka wani bidiyo a shafinshi na Instagram inda aka ganshi tare da sauran 'yan kwallon suna rawa tare da rera wakar godiya irin ta kirista.
Wani ya jawo hankalin Ahmed Musa akan cewa kar ya manta shifa musulmine.
Musa ya mayarmai da martanin cewa, to sai me kenan?
Mutumin ya kara da cewa, (wanda kake tare dasu) suna rawa da rera wakar kiristanci.
Ahmed Musa ya mayar mishi da martanin cewa, kada kazo shafina kana maganar addini, ka cire shi daga shafina ina yin abinda nikeso ne, ba kai zaka gayamin abinda zan yi ba. Ka barwa kanka idan baka son abinda nikeyi malam musulmi.
Post a Comment