A daren jiyane uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta gayyaci taurarin fina-finan Hausa da mawakan Hausa a fadar shugaban kasa inda aka kaddamar da waka ta musamman da aka yi dan yabon shugaban kasa, M. Buhari wadda akawa lakabi da Sakamakon Canji.

A jawabinshi a gurin taron, Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya bayyana cewa tunda suke babu gwamnatin da ta karramasu ta basu muhimmanci ta kuma nuna musu cewa suma mutanene masu bayar da gudummuwa ga al'umma kamar wannan gwamnati.
Adamun ya kuma godewa gwamnatin tarayya da irin wannan karamci da aka musu.

Ya bayyana cewa tunda yake be tafa tunanin zai taba tsayawa gaban uwargidan shugaban kasa haka yana magana ba dan haka babu abinda zasu ce sai godiya.
Daga nan kuma mawaka da 'yan fim suka hau kan dandamali inda aka fara rera wakar ta Sakamakon Canji.

Ana tsaka da wakarne sai shugaban kasa, M. Buhari ya shigo dakin taron da mukarrabanshi inda ya zauna ya kusa da uwargida, A'isha ya saurara suna murmushi tare kamin daga baya ya tashi ya fice daga gurin.

A jawabinta a gurin taron, uwargidan shugaban kasa, A'isha ta bayyana muhimmancin masu aikin nishadantarwa inda tace wakilan jama'a ne wanda suka zaba kuma suka kare kuri'unsu wanda a karshe yayi sanadiyyar lashe zaben shugaban kasa M. Buhari, ta bayyana cewa masu nishadantarwar suna mu'amala da miliyoyin mutane dan haka ta yi kira a garesu da su bayar da gudummawa wajan tallata zaman lafiya, hadin kai yaki da shan miyagun kwayoyi, hakuri da juna, yaki da safarar mutane, yaki da cin zarafin kananan yara dadai sauransu.

Ta tabbaya wakar ta Sakamakon Canji a matsayin wadda ta bayyana ayyukan alherin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yiwa kasar nan inda tace masu nishadantarwar sun taimaka wajan tallata manufar gwamnati da kuma koya wa mutane kyakkyawar dabi'a, dan hakane take karramasu.
Akwai me magana da yawun shugaba kasa, Garba Shehu da matar gwamnan Kogi da ta Kaduna da sauran manyan mutane da suka halarci wannan taro.

Daga cikin masana'antar fim din Hausa akwai, Adam A. Zango, Ado Isa Gwanja, Aminu Alan Waka, Nazifi Asnanic, Nazir Ahmad, Sarkin Waka, Saratu Gidado, Daso, Rabiu Rikadawa, Dila, Tindirkin Kano, Alasan Kwalle, Bakin Wake, Halima Atete, Fati Shu'uma, Adamu Hassan Nagudu, Rukayya Dawayya, Ibrahim Maishinku, Maryam Yahaya, Amal Umar, Hannatu Bashir, Fati Washa, Ali Jita, Jamila Umar Nagudu, Abubakar Sani, Fati Nijar, Hauwa Waraka, Abdu Boda, dadai sauransu duk sun halarci wannan taro.

Daga karshe uwargidan shugaban kasar ta bi kowannen su inda ta bashi lambar yabo ta gudummuwar da ya bayar wajan ci gaban masana'antar nishadi.





















Post a Comment

 
Top