Wata kotu a jihar Kano ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga ci gaba da binciken da ta fara kan zargin da ake yi wa Gwamnan jihar, Umar Ganduje na karbar rashawa daga 'yan kwangila.

A bangare daya kuma, Fitaccen malamin Addinin Musuluncin nan, sheikh Ibrahim Khalil ya aje mukaminsa na Mai Ba Gwamnan Kano shawara inda ake ganin matakin da malamin ya dauka bai rasa nasaba da zargin rashawa da ake yi wa Gwamnan jihar, Umar Ganduje.

Post a Comment

 
Top