Lokaci mai tsada kowa da Alkur'ani bude a gaban sa, wa zai iya rantsewa cewa lallai abinda ake yi adalci ne? Ba wanda zai iya rantsewa, amma kowa zai iya rantsewa cewa zalinci ake yi.

 To ya za a yi rayuwar mu ta yi kyau muna azzalumai? Sama azzalumai kasa azzalumai shikenan sai rayuwa ta yi kyau? 

Babu yadda za a yi mutane su ingantu haka kawai basu da shugabanci, babu kuwa ingantaccen shugabanci idan jahilai suka yi kane-kane akan karagar shugabanci. 

Dole sai wadanda sun san wani abu na addini, sun san wani abu na Ilimin rayuwa, suna da wani bangare na tsoron Allah tattare da su, sun kama ragamar mulkin Al'umma. 

Lokacin da suke mulki tsayawar su a gaban Allah su da SHI suke tunawa ba abinda za su sauka da shi ba. Ba abinda za su mallaka ba, ba abinda suke da shi a account din su na gida ko na waje ba. Tambayar da za a yi musu a gaban Allah da wannan suke kwantawa barci da wannan suke tashi. 

To sai an samu irin wadannan Shugabannin, wanda zai tashi ya je kasuwar kauye, ya je kasuwar birni, ya je shagunan da ake boye abinci ya kira Kwamishinan 'Yansanda, ya kira 'yan Mobayil, ya kira Daraktan SSS a fasa shagon a sayarwa da Talakawa abinci. 

Ba karya masa farashi za a yi ba, idan ya saya Naira 50 a sayar masa Naira 70 a ba shi kudinsa ko a sa masa a banki ba ya ci riba ba? 
Don Allah idan aka yi haka an zalince shi? An taimake shi duniya da lahira kuma an taimaki bayin Allah.

 Amma yanzu masifar da muke ciki fashi da makami, sace-sace, KOWA BARAWO, KOWA AZZALUMI ba fa Allah zai aiko da Mala'iku su gyara ba, mu ne za mu gyara mu Bil Adama. 

A duniya fa ba mu kadai ne muke rayuwa ba. A Afirka kadai kasashe nawa ne? Mu me ya sa muka zama daban? A duniya kasashe nawa ne? Don me sauran suke tafiya a tsari Mu ba mu da tsari? 

Don me daidai da waya ta GSM mutumin Nijar sai ya buga ta cikin kwanciyar rai kai dan Najeriya ba ka buga ta cikin kwanciyar rai ba? Don me mutumin Nijar hasken wutar lantarki ya samu cikin kwanciyar rai kai ba ka samu cikin kwanciyar rai? 

Ga Boda tazarar da ke tsakanin ka da Nijar wajen kilomita 1500 amma da ka shiga ba shi da matsalar ruwan famfo in an ce akwai da ka murda za ka ga ya zo. Kai kuma ace akwai famfo ka kunna babu. In an ce akwai lantarki ka kunna akwai. Kai kuma in an ce akwai lantarki ka kunna babu. 

Can Mutum nan Mutum, nan bakar fata can bakar fata. Ka ga sai an canja kenan. Najeriya ta ninka Nijar a kudi. A yau idan aka kadawa Nijar kararrawa aka ce za a sayar da ita, kila Najeriya ce za ta fara sayen ta. Kila ma mutum daya ya iya sayen ta. To shikenan jira kuke a kawo Mala'iku su sauya muku? 

Mu dai aikin mu mu fada muku. Ko Ku dauka ko ku yi dariya. Wannan ku ta shafa...

Allah Ya Jikan Sheikh Ja'afar Ya Gafarta Masa Dukkan Zunubansa. Allah Ya Karbi Shahadarsa.

Post a Comment

 
Top