Suna: Takaddama
Tsara Labari: Yakubu M. Kumo
Kamfani: JS Inuwa International Limited
Shiryawa: Mustafa Ahmad She she
Umarni: Ali Gumzak
Jarumai: Ali Nuhu, Aminu Sharif Momo, Abba Al-mustafa, Baballe Hayatu, Rabi’u Rikadawa, Nasir Naba, Isa A. Isa, Khalisat Mamza. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Hasanu (Aminu Sharif Momo) a cikin motar sa da daddare yana tafiya, cikin tukin ganganci ya take kafafun wani matashi wanda ya kwanta a waje don shan iska. Bayan Hasanu ya koma gida sai yagargadi mai gadin gidan akan kada ya saurari duk mutanen da za su zo don kawo karar sa. Lokacin da mahaifin yaron da aka takewa kafa yazo gidan su Hasanu ya tarar da mahaifin Hasanu wato Alhaji Bilya (Ali Nuhu) sai ya nuna bai yarda ba sai ya dau mataki akan abinda Hasanu yayiwa dan sa, jin hakan yasa Alhaji Bilya ya nuna shi yafi karfin duk wata hukuma ko yakai karar dan sa babu abinda za’a yi masa.
Haka kuwa mahaifin yaron yaje kotu ya shigar da kara amma ma’aikata suka nuna babu abinda za su iya akan haka saboda matsayin Alhaji Bilya (Ali Nuhu) ya wuce a zartar da hukuncin komai a kan sa. Haka mahaifin yaron yayi Allah ya isa ya tafi. Hasanu ya kasance mutum mara imani da ganin darajar kowa saboda yana takama da dukiyar mahaifin sa gami da matsayin mahaifin sa, hakan ne yasa yake yiwa kowa rashin mutunci kuma a zauna lafiya, akwai wani lokaci da ya tare wata budurwa yana yi mata magana (Khalisat Mamza) amma sai taki kulashi saboda rashin tarbiyyar sa, hakan ne yasa Hasanu (Aminu Sharif) ya mare ta kuma ya tada mata miyagun kalamai, bayan ta kuma gida ne ta sanar da iyayen ta irin cin mutuncin da Hasanu yayi mata a kan titi, nan fa mahaifin ta (Rabi’u Rikadawa) yaci alwashin daukar mataki akan hakan, amma bayan yazo gidan su Hasanu sai mahaifin Hasanu wato Alhaji Bilya ya nuna goyon bayan abinda dan sa ya aikata, hakan ne yasa suka yi sa’insa da mahaifin budurwar, sai dai bayan komawar sa gida jami’an tsaro suka zo suka kama sa gami da yi masa sharrin yake gidan Alhaji Bilya yaci mutuncin su, haka aka tafi dashi har sai da aka bata masa lokaci a hannun hukuma. Mahaifiyar Hasanu tana nuna rashin jin dadin ta akan abinda Hasanu ke aikatawa, amma sai mijinta Alhaji Bilya ya nuna hakan ba komai bane, ana cikin hakane wata rana dan uwan mahaifin Alhaji Bilya yazo wanda ya kasance babban malami, yana nuna masa rashin dacewar abinda dan sa yake yi, amma sai Alhaji Bilya bai dauki shawarwarin da ya basa ba, sai ma gargadi da yayi masa akan ya daina zuwa gidan sa matukar irin abinda zai dinga kawo sa kenan, Haka shima Hasanu ya wulakanta babban malamin wato dan uwan kakan sa, dakyar Alhaji Bilya ya janye Hasanu wanda ke kokarin dukan malamin yana fada masa miyagun kalamai. Wata rana Hasanu da abokan sa suna cikin club suna cashewa sai rigima ta hada shi da abokin sa Salisu (Nasir Naba) wanda ya nuna bai yarda duk rigimar da za su yi ya ci zarafin mahaifin sa ba, hakan ne ya fusata Hasanu har ya fasa kwalba zai rotsawa Salisu, amma sai dayan abokin nasa Nura (Abba El-Mustafa) ya shiga tsakanin su gami da bin bayan Hasanu wanda yayi fushi ya fita waje yana cin alwashin sai ya kashe Salisu, Nura ya rarrashi Hasanu akan yabar komai ya wuce, Hasanu ya nuna kamar komai ya wuce. Ai kuwa wata rana Hasanu tare da abokan sa Nura da Salisu suna cikin mota sai Hasanu ya tura Salisu ya bude bayan motar don kwaso masa wasu kudi da za su kashe.
Bayan fitar Salisu ya tsaya a bayan motar sai Hasanu yayi baya da motar yabi ta kan Salisu ya kashe shi, ganin hakan ne ya firgita Nura tsoro ya kama shi ya soma rokar Hasanu akan kada shima ya kashe shi, amma sai Hasanu ya nuna bazai masa komai ba idan ya rufe bakin sa, haka shima mahaifin Hasanu ya goyi da bayan kisan kan da dan sa yayi kuma ya sake gargadin abokin sa akan kada ya sanar da duniya abinda Hasanu ya aikata. Sai dai kuma Nura ya kasa nutsuwa kullum cikin fargaba yake, hakan ce yasa wata rana da yayi wani mugun mafarki ya furta a bayyane cewar shi ya kashe Hasanu, jin hakan ne yasa yayan sa yaje ya sanar da yayan Salisu wanda ya dawo daga aikin soja (Baballe Hayatu) jin hakan ne yasa suka sanar da hukuma, kafin wani lokaci an kama Hasanu ana tuhumar sa, sai dai mahaifin sa ya soma fafutukar fitar dashi wanda har ya kori babban jami’in tsaron dake bibiyar yadda lamarin ya afku, ganin kamar Hasanu zai iya kubuta daga hannun hukuma sai yayan Salisu da sauran magoya bayan sa suka soma neman taimakon hukumar kare hakkin dan Adam gami da neman goyon bayan jama’a don kawo karshen zaluncin Hasanu, hakan ce tasa bayan an shiga kotu alkali wanda Alhaji Bilya ya bashi kudi me yawa don a fidda dan sa, sai Alkali ya kasa yanke hukunci saboda tsoron kada yayi ha’inci ya rasa aikin sa, daga karshe kuma ya mayarwa da Alhaji Bilya kudin sa kuma aka yankewa Hasanu hukunci ta hanyar rataya. Faruwar hakan ce tasa Alhaji Bilya ya kamu da ciwon zuciya yayin da su kuma wadanda yayi silar korar su daga aiki aka mayar da su kan aikin su shi kuma Hasanu aka rataye shi.
Abubuwan Birgewa:
1- Fim din ya fadakar kuma ya nishadantar, gami da rike me kallo, kuma labarin ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba.
2- Daraktan yayi matukar kokari wajen tafiyar da labarin ta hanyar da ta dace ba tare da an dakushe karfin sa ba.
3- An samar da wuraren da suka dace da labarin wato (Locations)
4-Jaruman sun yi kokari wajen taka rawar da ta dace, musamman Hasanu (Aminu Sharif) wanda yaja fim din.
5- An samar da kayan aiki masu kyau, musamman Camera, sauti ma ya fita radau, haka me yin kwalliya (Make-up) yayi kokari wajen aikin sa.
Kurakurai:
1- Ya dace a rubuta sunan fim din gaba daya da haruffan Hausa, wato Takaddama, saboda an nuna bahaushen labari ne kuma da yaren Hausa aka yi sa.
2- Lokacin da Nura (Abba Al-mustafa) ya hadu da yayan Salisu (Baballe Hayatu) a wajen jana’izar Salisu, me kallo yaji lokacin da Nura (Abba Al-mustafa) yace wa yayan Salisu, “yaya Nura ashe ka samu zuwa?” Tunda an nuna wa me kallo cewa (Abba Al-mustafa) shine Nura. Shin sunan su daya kenan da yayan Salisu?
3- Lokacin da jami’an tsaro suka je tafiya da (Rabi’u Rikadawa) bai kamata su shiga gidan sa kai tsaye ba tare da nuna shaidar da ta ba su damar yin hakan ba, ya dace su jira sa a kofar gida ko kuma a samar da wani dalilin na shigar su cikin gidan, haka kuma bai kamata su tsaya fadar laifin da ya aikata tun a cikin gidan ba, ya dace su bari har sai an je ofis su yi bayani.
4- Abin daukar sauti ya fito (boom mic) a lokacin da Musa yayan Nura yaje ya wajen zaman makoki ya sanar da (Baballe Hayatu) cewar Hasanu ne ya kashe Salisu.
5- Lokacin da babban malami dan uwan mahaifin Alhaji Bilya yaje ya yiwa Alhaji Bilya Nasiha, bayan fitowar sa kofar gida me gadin gidan ya tare sa a waje yace yaga ya fito yana kuka, sai dai kuma a fuskar malamin babu ko kwalla balantana hawaye, haka kuma babu alamun da suka nuna cewar kuka yake sabanin yadda me gadin ya fada.
6- Lokacin da Alhaji Bilya yake fadawa matar sa cewar sai dai su fara shirin daukar dangana domin yaje gidan alkali yaga babu alamun nasara. Bayan Alhaji Bilya ya mike tsaye abin daukar sauti (boom mic) ya fito a saman hular sa.
Karkarewa:
Fim din ya fadakar kuma an yi kokarin isar da muhimmin sako me amfanarwa, musamman ga iyayen da ke sangarta ‘ya’yan su wadanda ba sa son laifin ‘ya’yan na su, da kuma wasu ‘ya’yan manyan masu takama da matsayin iyayen su wajen wulakanta al’umma. Tabbas an yi kokarin isar da sakon da zai zamo darasi ga al’umma.

Post a Comment