Suna: Adamun Adama

 Tsara Labari: Munzali M. Bichi

 Kamfani: Sai Na Dawo Film Production

 Shiryawa: Yahuza Sai Na Dawo 

Umarni: Sadik N. Mafia 

Jarumai: Adam A. Zango, Aisha Aliyu Tsamiya, Falalu A. Dorayi, Isah Adam, Abdul M. Sharif, Nuhu Abdullahi, Magaji Mijin Yawa, Hauwa Maina, Fati S.U, Fatima Abubakar. Da sauran su. Sharhi: Hamza Gambo Umar   A farkon fim din an nuna Alhaji Sa’ad tare da italan sa, babban dan sa Kabir (Isah Adam) da matar sa (Hauwa Maina) suna taya ‘yar su Adama (Aisha Aliyu Tsamiya) murnar zagayowar ranar haihuwar ta, a sannan ne mahaifinta ya dinga yabon halayen ta. Daga bisani kuma mahaifin ta ya dage akan lallai sai ta fito da mijin aure, dalilin hakan ne yasa ya turo mata dan gwamna (Abdul M. Sharif) don su fuskanci juna kana su yi aure, amma sai Adama ta nuna sam bai yi mata ba kuma bata ra’ayin aure karatu ne a gaban ta. Bayan ta kori dan gwamna sai mahaifin ta ya sake nemar mata auren dan sarki, amma shima bayan zuwan sa ta nuna ba aure bane a gaban ta kuma ba ta son shi. Hakan ya sa mahaifin ta Alhaji Sa’ad ya nuna mata fushin sa sosai, haka itama mahaifiyar ta tun tana goyon bayan ta har ta zare hannun ta akan abin. Adama ta ci gaba da korar manema auren ta, daga cikin masu zuwa har da wani fitaccen mai kudi (Nuhu Abdullahi) Wanda shima ya nuna da gaske auren ta yake son yi amma shima ta wulakanta sa. Wata rana ta fito harabar gidan su tana tunani akan wani aiki da aka bata a makaranta wato (Assignment) amma ta kasa yi, sai mai gadin gidan wato Adamu (Adam A. Zango) ya ganta kuma ya nuna zai iya yi mata aikin, nan fa ta bashi kuma cikin sa’a yayi mata aikin daidai, tun daga sannan ta ci gaba da kawo masa aiki yana yi mata, yayin da shi kuma ashe soyayyar ta tayi wa zuciyar sa kamun kazar kuku, hakan ne yasa yayi amfani da damar nuna mata soyayyar sa ta hanyar aika mata da sakonni ta wayar ta, tun Adama tana ganin wasikun soyayya tana gogewa daga cikin wayar tata, har ta soma jin dadin kalaman nasa ta soma mayar masa da martanin kalamai masu sanyaya zuciya irin nasa. Daga bisani kuma har shakuwar Adama da Adamu mai gadi yayi karfi suka fara yin waya suna soyayya ba tare da ta gane cewar da mai gadin gidan su take soyayya ba, sun yi nisa sosai a soyayya har sun tsara lokacin da zasu hadu, wanda hakan ne yasa Adama tabkarbi kudi a wajen iyayen ta ta dinka sababbin kayan sawa masu tsada sannan kuma ta kira Adamu mai gadin ya dauke ta a mota it’s da kawar ta (Fati S.U) ya kai su babban kanti suka yi siyayyar kayan ciye-ciye wanda zasu tari bakon su da shi, ganin hakan ne yasa jikin Adamu ya soma yin sanyi saboda ganin yadda Adama take rawar jiki a kansa, kwatsam ana cikin haka sai wani saurayi yazo hira wajen Adama, amma saboda ba shi da tarin abin duniya sai mahaifin ta ya wulakanta sa ya koresa. Ganin hakan ne yasa jikin Adamu ya kara yin sanyi gami da tunanin Adama ba abokiyar auren shi bace, hakan ne yasa yaje wajen tsohon saurayin ta (Nuhu Abdullahi) ya nuna mishi cewar ya sadaukar masa da soyayyar Adama yana so yaje wajen ta a matsayin shine wanda suke hira. Bayan Adamu ya gama tsara hakan ne ya hada kayan sa gami da yin karyar cewar mahaifiyar sa bata da lafiya ya tafi kauyen su. Tafiyar Adamu babu jimawa sai tsohon saurayin Adama ya dawo a matsayin shine wanda suke yin waya. Sai dai tun ba’a yi nisa ba Adama ta gane cewar ba shi bane, bayan sun rabu kuma ta ci gaba da kiran wayar Adamu amma bata same shi ba. Hakan ne ya tashi hankalin ta har ta fara rashin lafiya, yayin da mahaifin ta yasa a bincika mata me lambar wayar da ya jefa ‘yar sa cikin tarkon soyayya. Shi kuwa Adamu bayan ya koma kauyen su sai tsohuwar budurwar sa Uwani (Maryam Yahya) ta dage akan lallai sai ya aure ya, amma sai yaki amincewa da bukatar sa saboda wasu dalilai wanda suka sa bazai iya auren ta ba. Yana zaune a kauyen har zuwa wata rana da abokin sa yaga tsohon layin wayar Adamu a bayan waya sai ya dauka ta dora akan waya, faruwar hakan ce tasa masu binciken da mahaifin Adama ya saka suka gane kauyen da me wayar yake, nan fa suka biyo bayan Adamu suka kamashi suka damka shi ga hukuma aka soma tuhumar sa har daga karshe aka gane cewar shine yake soyayya da Adama. Yayin da Adama ta amince zata aure shi a duk yadda yake, haka mahaifin ta ma ya amince zai aura mata shi saboda yana son abinda take so. 
  
.Abubuwan Birgewa:

 1- Labarin ya nishadantar, musamman ga ma’abota son kallon fim din soyayya.

 2- An yi kokarin samar da wuraren da suka dace da labarin.

 3- Kalaman Jaruman sun yi dadi, wato (dialogue)

 4- Camera ta fita radau, sauti ma babu laifi.   


Kurakurai: 

1- Lokacin da aka nuna Dan Gwamna (Abdul M. Sharif) yazo hira wajen Adama, kayan jikin sa sam bai dace da matsayin sa da aka nuna ba. Tun da an nuna cewar shi dan gwamna ne kuma matashi mai takama da nuna isa, ya dace ace sutturar dake jikin sa ta zamo mai tsada wadda zata kara bayyana matsayin sa.

 2- A farkon fim din lokacin da iyayen Adama suke tayata murnar zagayowar ranar haihuwar ta, me kallo yaji mahaifin ta yana yabon kyawun halin ta da tarbiyyar ta, amma daga bisani kuma sai aka ga sam Adama bata biyayya akan umarnin mahaifin na ta, domin ya turo mata mazajen aure, Dan Gwamna da Dan Sarki don ta zabi gwanin ta, amma sai Adama taki yi masa biyayya domin bata nuna girmamawa ga wadanda mahaifin ta ya hada ta dasu ba, sai ma wulakanta su da tayi. 

3- Me kallo yaji Adama tana ikirarin cewa karatun ta yafi duk wata soyayya, amma sai ga shi har fim din ya kare ba’a ga Adama ta fita da nufin zuwa makaranta ko kuma ta dawo daga makarantar ba. Ya dace ko sau daya ne a nuna taje makarantar ko kuma ta dawo. Idan kuma a gida take yin nata karatun to ya dace a bayyana hakan kamar yadda aka bayyana me gadi yana koya mata (assignment) wanda aka bata a makaranta.

 4-  Kwatsam sai aka ga Bawa (Falalu A. Dorayi) yaje ziyara kauyen su Adamu da nufin ya duba mahaifiyar Adamu wadda yake zaton ba ta da lafiya, shin dama Bawa yasan kauyen su Adamun ne? Tunda a baya ba’a nuna Adamu  ya kwatanta masa kauyen ba, to ya dace a samar da wata hanyar ta zuwan na sa, ko da ta hanyar nuna cewar sun zo tare da jami’an tsaron da suka zo kama Adamu ne.

 5- Bayan Adamu ya nisanta kan sa da Adama, me kallo yaji mahaifin Adama yace ta kimtsa don ya shirya mata tafiya zuwa kasar holand don ta huta, shin Adama ta gama karatu ne da har zata tsallaka zuwa wata kasar? Idan kuma bata gama ba ya makomar karatun nata yake? Haka kuma idan hutu aka yi musu a makaranta wanda hakan zai iya bata damar zuwa wata kasar to ya dace a fahimtar da mai kallo don a fiddashi daga wasu-wasi. 

6- Lokacin da Adama taje babban kanti (super market) don yin siyayya, bayan ta biya kudi ta dauki ledoji zata fita, an sake maimaita wajen har karo biyu. Shin me ake son a nuna wa me kallo a game da maimaicin scene din?

 7- Bayan jami’an tsaro sun je kauyen su Adamu sun kama su shi da abokan sa gami da kwace wayoyin hannun su, me kallo yaga kabiru (Isah Adam) ya sake dawowa neman Adamu shi da wasu jami’an tsaron, har ma suka bi sa cikin daji suka kama shi, shin dama a baya da suka kama shi basu tafi dashi bane? Idan kuma jami’an tsaron sun tafi dashi a farkon zuwan su kauyen, shin sakin sa suka yi tun kafin hukuma ta gama binciken ta a kan sa? Ya dace a samar da dalilin sake dawowar jami’an tsaro cikin kauyen ko don a tabbatar da ingancin zahirin aikin hukuma, ta yadda mai kallo zai gamsu da hasashen cewa zahiri fa yake gani ba wai fim ba.  

 Karkarewa: 

An yi kokarin nuna tasiri gami da karfin soyayya, sai dai kuma labarin ya tafi a tsaye babu doro, haka kuma babu muhimmin sako, ko kuma wani darasi me karfi wanda fim din yake koyarwa. Wallahi a’alamu!.

Sources:leadershipayau.com

Post a Comment

 
Top