Rigima da ya kai ga tashin hankali tsakanin wasu kungiyoyin asiri guda biyu a yankin Choba na jihar Rivers ya yi sanadin mutuwar wasu matasa biyu.

Mazauna wannan yanki sun wayi gari suka gan gawakin wasu matasa biyu tsirara kuma hannayensu daure a bayan su, bayan an gundule kansu sai aka saka a cikin laida aka ajiye a gefen titi.

Jama'ar wannan unguwa sun yi kira ga jami'an tsaro su kawo masu agajin gaggawa domin hana harin daukar fansa daga bangaren kungiyar asiri da aka kashe mutanensu.

Harkar tashin hankali da ke kaiwa ga kashe kashe  ya zama ruwan darec a jihar Rivers, domin yan watanni da suka gabata an kashe fiye da mutum biyar a wani tashin hankali tsakanin kungiyoyin asiri a cikin al'ummar Omerelu da ke karamar hukumar Ikwerre a jihar Rivers.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top