Wadannan wasu 'yan matan makarantar sakandaren Isolo Senior Secondary School dake jihar Lagos, shugaban makarantar (principal) me suna Mrs J.O Sadare ta kore su daga makaranta a jiya Laraba saboda sun saka hijabi.

Kuma saboda rashin mutunci har da rubuta takarda na dakatarwa (suspension letter) ta baiwa daliban, a cikin daliban da aka kora saboda sun saka hijabi har da mataimakiyar head girl na makarantar.

Ina kungiyoyin kare hakkin musulmi na Nigeria? Wannan babban kalubale ne gareku, hakki ya rataya a wuyanku ku baza manyan lauyoyinku su samarwa mata musulmi 'yan makarantar sakandare a jihar Lagos 'yancin saka hijabi.

Wannan tauye hakkin musulmai ne, da rashin biyayya wa dokokin tsarin constitution na Kasa wanda yake kan gaba da kowace doka a Nigeria, tunda anyi tanadin bada 'yanci ga kowani 'dan Nigeria yayi irin addinin da ya ga dama batare da tsangwama ba matukar bai ci karo da zaman lafiyar Nijeriya ba.

Muna fatan a yi wa musulmai adalci a makarantun firamari da na sakandire a jihar Lagos, ko a cikin addinin kiristanci saka hijabi wajibi ne ba wai ganin dama ba, akwai a rubuce cikin littafin Injil, to amma da yake kiristoci 'yan tawaye ne (protestant), sun yiwa addininsu tawaye basa bin karantarwan Littafinsu sun gina addininsu akan son rai da son zuciya da tunanin hankalinsu, wannan ba dalili bane da zaisa a mayar da musulmi dabbobi marassa mutunci da basa yiwa addini biyayya kamar su ba!

Allah Ya sauwake.

Rariya.

Post a Comment

 
Top