Fusatattun jama'a sun afka ma wani matashi mai suna Prince Tetteh dan shekara 24 da duka bayan sun zarge shi da satar wani babur a Nkurakan da ke Yilo Krobo a gabacin kasar Ghana, lamari da ya kai ga mutuwarsa nan take.

Abokin aikata satar nashi ya tsira, domin dai da ya samu ya arce da gudu, an kasa kama shi, amma sai Prince ya gamu da rashin sa'ar ajali, kumma aka kama shi, daga bisani jama'a suka aika shi barzahu da duka.

Kakakin yansanda na gundumar gabacin Koforidua DSP Ebenezer Tetteh ya tabbatar da faruwar lamarin .

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top