Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi dauki akan zargin cewa rayuwarsa da na iyalinsa na cikin hatsari.


A wani wasika da ya aikewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, mai kwanan wata 7 ga watan Satumba, 2018, Atiku ya alakanta zargin barazanar ga kudirinsa na takarar kujeran shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

An tura kwafin wasikar ga shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya bukaci Shugaba Buhari da yayi gaggawan bincikar zargin.

Ya bayar da lambar mai yi masu barazanar a matsayin 08148228704.

Atiku ya bukaci shugaba Buhari da ya bashi Karin yan sanda da zasu bashi kariya tare da iyalinsa.

Atiku ya bayyana cewa matarsa da ýarsa sun samu wasikar waya daban-daban daga wani lambar waya, inda aka bukaci ya daina takaran kujerar shugaban kasa, cewa idan yaki za’a yi masu fyade tare da kashe su.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa marubucin wasikun barazanan ya bayyana cewa suna lura da duk wani motsi na iyalan nasa.

Ya bukaci Shugaban kasa da ya binciki lamarin domin idan har aka aikata hakan yana iya zama babban kalubale ga tsaron kasar.
Naija.ng

Post a Comment

 
Top