Wasu gungun 'yan daba sun kai farmaki sakatariyar jam'iyyar APC da ke karamar hukumar Okitipupa na jihar Ondo inda su kayi kaca-kaca da kayayakin aiki tare da tarwatsa dukkan mutanen da ke sakatariyar.
Kamfanin dillanci labarai NAN ta ruwaito cewa 'yan daban sun lalata kone tutan jam'iyyar tare da yaga fostocin 'yan takarar kujerun Ciyaman, Kansiloli da shugabanin gunduma na jam'iyyar da ke sakatariyar.


Wani wanda abin ya faru a idanunsa amma ya nemi a sakayya sunansa ya fadawa NAN cewa farmakin da 'yan daban su kawo ba zai rasa nasaba da zargin canja sunayen deleget na wasu gundumomi da ake jita-jitar cewa anyi a jihar.

Ya kuma ce 'yan daban sunyi gargadin cewa ba za'a taba samun kwanciyar hankali ba muddin ba'a mayar da sunayen deleget din da jama'a suka bayar a gundumomi ba.

A bangarensa, Ciyaman din APC na karamar hukumar Okitipupa, Mr Bode Ikulala, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ya shaidawa NAN cewa jam'iyyar bata fitar da sunayen deleget ba lokacin da aka kai harin.

Ya kara da cewa dukkan wadanda suke da wata korafi su shigar da kara ta hanyar da ya dace a maimakon tayar da rikici da daukan doka a hannunsu.

Ikulala ya ce yanzu hankula sun kwanta a Okitipupa bayan ya sanar da jami'an 'yan sanda inda abinda ke faruwa a sakatariyar.

Read more at: https://ift.tt/2wMX8h0

Post a Comment

 
Top