Yan sanda sun cafke wani malamin addini, Pentecost Ewa Usang, a birnin Calabar a jihar Ribas a kan zargin yiwa wata ‘yar shekaru 8 fyade.


Malamin addinin ya ce shi ke jagorantar cocin Christ Glorious Assembly a babban birnin jihar Ribas, Calabar.


Ya fadawa manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda cewa aikin shaidan ne ya sa shi aikata wannan abun kunyar.

Ya bayyana hakan ne mintuna kadan bayan kwamishinan ‘yan sanda resheh jihar Ribas, Mr. Mohammed Inuwa Hafiz, ya gabatar da shi a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda.

“Ina nan ne a kan zargin bata budurcin wata ‘yan karamar yarinya, suna na Pentecost Ewa Usang, na kasance malamin addinin cocin Christ Glorious Assembly da ke Calabar.

“Shaidan ne ya sa ni aikata wannan mummunar aiki kafin na dawo haiyaci na san abunda ni ke ciki na aikata aikin, ba ni na aikata wannan mummunar aikin ba.

“Ina kusa da yarinyar sannan kafin abun ya faru, na dawo haiyaci na sannan ban bar abun ya faru ba, yarinyar ‘yar asalin kasar Kamaru ce,” ya ce.


Sauran laifukan da suka shafi fyade da lalata budurcin mata inji kwamishinan ‘yan sanda, ya ce ya faru ne a unguwar Akamkpa inda wani matashi, Ubong Umoh, ya yiwa wata yarinya ‘yar shekaru 7, Victory Goodness Sunday.

Dayan kuma ya faru ne a kauyen Edem Esa Abakot da ke Akpabuyo inda wani malamin addini cocin Jesus is Barrister in Zion Church, Daniel Asuquo Udoh, ya lalata budurcin wata yarinya ‘yar shekaru 7, Rachel Dominic, ta hanyar yi ma ta fyade.


Kwamishinan ya ce ” a 22 ga watan Satumba 2018, da misalin karfe 3:45 na yamma, wata tawagar ‘yan sanda da ke aiki karkashin ofishin ‘yan sanda da ke State Housig Division sun cafke wani matashi, Emmanuel Bassey, dan shekaru 35 wanda ake zargi da aikata fyade a gida mai lamba 35 a birnin Calabar bayan sun samu bayanin ya aikata fyaden.

“Shi wanda ake zargi an samu labarin cewa ya dauke wata ma’aikaciyyarsa ‘yar shekaru 18, a wannan ranar da misalin karfe 8:300 na safe a gida mai wannan addireshen inda yayi amfani da iya karfensa ya yaga ma ta tufafinta sannan yayi ma ta fyade.

“Yarinyar da aka yiwa fyade a nan take ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da ita zuwa asibiti ‘yan sanda domin likitoci su duba lafiyar jikinta.

Shi wanda ake zargi ya furta aikata laifin da ake zarginsa da shi sannan za a caje shi zuwa kotu da zaran ‘yan sanda sun gama gudanar da binciken su a kan lamarin,” Kwamishinan ya ce.

Hotunan su a kasa:


from Arewarmu | Best Arewa Entertainment and News Blog https://ift.tt/2CooUWI

Post a Comment

 
Top