Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke neman tikitin tsayawa takara a zaben shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP, Attahiru Bafarawa ya bayyana gwamnatin Muhammadu Buhari a matsayin musiba, in da ya ce, PDP za ta kawar da gwamnatin a zaben 2019.


Bafarawa wanda ya yi gwamna har sau biyu a Sokoto, ya kuma ce, Najeriya na fama da rashin lafiya ne saboda jagorancin kasar ba shi da lafiya.

Tsohon gwamnan na magana ne ga manema labarai a ranar Laraba a birnin Abeokuta, jim kadan da gabatar da jawabi ga jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Ogun, a wani mataki na ci gaba da yakin neman samun tikitin tsayawa takara.

A cewar Bafarawa, ba za su lamunci ci gaba da ganin halin da Najeriya ke ciki ba karkashin jagorancin shugaba Buhari kuma ya ce, za su hada kansu a jam’iyyar PDP don ganin bayan gwamnatin Buhari a zabe mai zuwa.

Bafarawa ya kara da cewa, jam’iyyarsa ba za ta yi wa wani bita da kullin siyasa ba muddin ta lashe zaben na shekara mai zuwa, domin kuwa za ta mayar da hankalinta ne kan gina kasar.
RFIhausa.

Post a Comment

 
Top