Hanyoyi mafiya sauki na rabuwa da amosanin kai (0 Likes) Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. 

Wadansu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana mata! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan matsala ta amosanin kai. A ciki akwai ganyen kashu da lemun tsami da ruwan kwakwa da kuma kwallon mangwaro. Shin ko kun san cewa ganyen kashu na maganin amosanin ka? To ga yadda za a sarrafa shi. 

 A wanke ganyen kashu sannan sai a daka shi a kwaba da ruwa. • Bayan haka, sai a shafa a fatar kai a bari na tsawon rabin awa kafin a wanke. Za a iya yin haka har na tsawon mako biyu insha Allah za a samu saukin amosanin ka. Ko kun san cewa lemun tsami ma yana warkar da amosanin ka, musamman idan an hada shi da ruwan kwakwa? 

A samu lemun tsami sai a matse ruwan, sannan a hada da ruwan kwakwa. • Sannan a shafa a fatar ka a jira na tsawon rabin awa kafin a wanke. Kwallon mangwaro na mangance amosanin ka. Kuma ana iya hada shi ne da madarar ‘butter milk’ kamar haka; • A busar da kwallon mangwaro, bayan ya bushe, sannan a daka. 

Za a iya kwaba garin kwallon mangwaro da ruwa sannan a shafa a kai ko kuma da madarar ‘butter milk’ sannan a shafa a fatar kai. Bayan minti 30 sai a wanke. Ana yi a kai-a-kai domin harkar fata sai a hankali ake samun sauki. . 

Copyright @aminiya

Zaku iya tambaya ta hanyar comment.

👉👉Ku kasance da shafinmu www.trustposts.com donjin dadinku a koda yaushe...

Post a Comment

 
Top