Wata shakuwa da ake zargin tuni ta rikide ta koma soyayya mai karfi ta shiga tsakanin daya daga cikin matasan jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood dake tasowa, wato Maryam Yahaya da wani mashiryin shirin fina-finai, Abubakar Bashir Maishadda.

Masu bibiyar harkokin dake gudana a masana'antar fina-finan ta Hausa dai musamman ma a bayan fage sun tabbatar mana da cewa a 'yan watannin nan wata alaka mai karfi da ake tunanin soyayya ce ta shiga tsakanin mutanen biyu.

A wani dan binciken da muka gudanar mun gano cewa kusan dukkan fina-finan da mashiryin fim din ke fitar wa akwai jarumar a ciki kuma ma takan taka muhimmiyar rawa a ciki.

Haka zalika ma dai soyayyar tasu ta kara fitowa fili karara ne a ranar 14 ga watan Satumba inda aka tsinkayi jarumar Maryam ta dora wasu hotuna a shafinta na dandalin zumuntar zamani na Instagram ita da Furodusa Maishadda sanye da zobuna iri daya wanda daga baya ta gogesu.

Maryam Yahaya dai na daya daga cikin jarumai mata dake tashe yanzu a masana'antar Kannywood tun bayan wata muhimmiyar rawa da ta taka a cikin shirin fim din Mansoor.

@Nigeriarmu Ayau

Post a Comment

 
Top