Fati Nayo ‘yar Fulanin asali, hazikar mace mai rike da sana’o’i daban-daban, kuma fitacciyar jaruma cikin shirin fim din Dadin kowa da take fitowa a Dillaliya, ta shawarci matan da suke harkar fim da su yi aure idan sun samu mazaje. Fati Nayo ta ba da wannan shawara ce, cikin tattaunawarsu da wakiliyar LEADERSHIP AYAU Lahadi, ga yadda hirar ta kasance.
Masu karatu za su so su ji cikaken sunanki da cikaken tarihin rayuwarki Sunana Fati Nayo fulanin Asali ce. Wadda aka fi sani da Kyauta Dillaliya a cikin shirin Dadin kowa Sabon salo, An haife ni a Kasar Saudi Arabia, a garin Madina, na yi karatu a Gombe, ina aiki a asibitin Murtala.
Kuma yanzu Ina wasan kwaikayo a Tashar Arewa 24 bangaren Dadin kowa Sabon salo. Ina yin Dj, da Humra, Dinkin labulaye, Ina kuma yi wa Ma’aurata nasiha, sannan ina yi wa yara tarbiya, ina yin waka – jefi, kazalika Ina yin dinkin kaya. Aikin Asibiti, Soja, waka, Dinki, wasan kwaikwayo, abu 5 suka ginu a zuciyata tun ina karama, har na girma, amma yanzu na samu 4 Soja ne ban samuba, da ma shi ma sojan ba ni zan yi ba, kawai suna birge ni don su Jarumai ne, kuma har yau ina kaunar Soja.
Shin menene ya ja ra’ayinki kika zabi yin wasan kwaikwayo alhalin kina aikin asibiti, kuma Kina da sa na’ar hannu ta dinkin labule? Film gaskiya tun ina karama nake sha’awar film, na kan tara kannena muna wasan kwaikayo, don haka da shi na tashi. Aikin asibiti kuwa kowa ya san albashi na sai karshen wata, wani watan kafin ya zo ka cinye su.
Dinkin Labulaye kuwa wata ran a samu wata ran kuma babu dinkin, sannan kuma ina da masu taya ni dinkin labulen idan ya samu. Aikin asibiti kuwa, wata ran wataran da safe, wata rana da dare wataran kuma hutu, Kinga ina da lokuta. Mun ji kin ce kina Dj na biki da nasihar ma’aurata da tarbiyar yara, shin ta yaya kike hada dawainiyar aikinki na asibiti da sauran ayyukanki? DJ yawanci sai da yamma, ko da daddare muke zuwa, kuma an fi yi Juma’a, Asabar, Lahadi.
Nasihar ma’aurata kuma idan na dawo daga aikin safe sai su zo su same ni, ai ita nasihar magana ce da baki, haka ma tarbiyar yara ita ma magana ce, don haka duk abinda ka dauka da sauki to zai zamo da saukin, haka ma Idan ka dauki abu da wahala to dole wahalar zai zamo maka.
Dalilin yawan sana’ata ita ce Wallahi ina da dangin mahaifiyata da yawa, a Gombe haka ma dangin mahaifina suna da yawa a Tudunwadar dan kade, kuma ina da dangin mahaifina a Rano, suma suna da yawa, don dangin babana ban san yawansu ba.
Kuma kowa so yake na yi masa, shi ne dalilin yawan sana’ata, ga kuma yara da ‘yan ‘uwa da muke ciki daya da ‘yan uba, da abokan arziki, don ni Wallahi ko tafiya nake a kan hanya idan na ga wasu sai kawai na ji ina ma ina da kudi na ba su, ga irin su Wasilan Kaduna suma da da kudin sai a yi wa yaransu kayan sallah. Kuma yanzu haka ma Ina son bude gidan abinci, in Allah ya yarda.
Sai da na yi wa Malam Daurawa magana ina son in dinga zuwa Rugagen Fulani don In dinga koya musu Karatun Islamiya, kin san ba su da Islamiyya. Ya ce to, kin san su ma Malamai abubuwa suna musu yawa, Allah ya sa mu dace. Kin ce kina sha’awar aikin soja don Suna burge ki wace shawara za ki ba wa mata masu aikin soja? Gaskiya Soja na burge ni, shawarar ita ce, a duk in da suke su rike addininsu, Ina kuma yi musu fatan Alkhairi.
Wace shawara Za ki ba wa mata masu sha’awar shiga harkar Fim? Shawarar ita ce, su yi aure, amma idan Allah ya kaddara sai sun yi to Shike nan, sai su tsarkake zuciyar su, su kuma rike Sallah, idan kuma suka samu Mijin aure nagari to su yi aurensu, don su sami ‘ya’ya nagari.
Wane kira za ki yi ga mata matasa da matan aure masu shaye-shaye Allah ya shirye su, kuma su ji tsoron Allah, sannan su kiyaye lafiyarsu, don shi shaye-shaye ba talauci ba ne, ba kuma kudi ba ne, kuma yana rage tunani mai kyau, sannan yana haddasa man tuwa. ‘Ya’yan talakawa suna yi, ‘Ya’yan masu kudi suna yi, ‘yan kauye na yi, Kai a yanzu Fulanin daji ma suna yi, Allah ya shirye mu baki daya.
Copyright @leadershipayau
Post a Comment