Tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya bayyana cewa shima ya yi na’am da ra’ayin a sake fasalin kasar nan wadda yana daga cikin abin da zai fi maida hankali a kai idan ya zama shugaban kasar nan.



Tambuwal ya fadi haka ne da yake ganawa da wakilan jam’iyyar PDP a Ado Ekiti, hedikwatar jihar Ekiti.


” Ba zan gudanar da mulki da nuna bangaranci ba kamar yadda gwamnatin Buhari ke nuna burbudin haka.


Ya kara da cewa babban dalilin da ya sa ya fito takarar shugabancin Najeriya shine ganin yadda wannan gwamnati ke nuna bangaranci da koma baya da aka samu a kasar tun bayan kafa wannan gwamnati.


” Babban abin da ‘ yan Najeriya zasu maida hankali a kai yanzu shine yadda za a jawo hankulan mutane su zabi mutanen da ke da kishin kasa ne ba nuna bangaranci, ko kuma yin amfani da banbanci na addini da kabilanci wajen raba kawunan kasa.


” Kowa na da masanoiyar yadda wannan gwamnati ke yin amfani da karfin iko na ta wajen bankare mutane da karfin tsiya da yin karfafa don ta zarce a 2019 da karfin tsiya.


Tambuwal ya jaddada cewa tabbas, babban abin da zai fi maida hankali a kai shine yadda za a sake fasalin kasar nan ta inda kowa zai yi na’am da.


” Da ya ke tofa albarkacin bakin sa a wajen taron, gwamna mai barin gado, Ayo Fayose ya kalubalanci Tambuwal da ya tabbata su da suka wanke Buhari tas suka saka masa rigar mutunci a 2015 har ya ci zabe, suyi duk abin da za suyi a 2019 su kwabe wannan riga.


Premiumtimeshausa.


Post a Comment

 
Top