Wasu jami'an hukumar FRSC a jihar Anambra sun gamu da wulakanci a hannun wasu fusatattun jama'a bayan an yi zargin cewa jami'an FRSC ne suka haddasa wani hadari da ya yi sanadin rauni ga fasinjojin wasu motoci guda biyu da suka yi hadari ciki har da wata mace mai juna biyu.

Majiyarmu ta ce jami'an FRSC din da ke gudanar da aikin sintiri, sun biyo wata mota ce a guje, sakamakon haka kuma aka yi taho mu gama da wata motar fasinja, lamari da ya haifar da wannan hadari.

Fusatattun jama'a da ke wurin sun kama wasu jami'ai na FRSC guda biyu da ke gudanar da sintirin, kuma suka wulakanta su a bainar jama'a, har da tilasta su zama a kasa bayan sun sha duka.

Daga karshe wani jami'in dansanda ya zo ya kuma ya nemi jama'a su daina dukan jami'an na FRSC. An garzaya Asibiti da wadanda suka sami raunuka.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top