Yayin da zabukan gama-gari na shekarar 2019 ke kara matsowa, kusan a iya cewa duk wani dan siyasa yanzu hankalin sa ya karkata ne a can bangaren.


Kamar dai yadda aka zata, masana harkokin siyasa da masu sharhi akan al'amurran yau da kullum a ko da yaushe sukan dauki lokaci suna bincike sannan kuma su bayyanawa jama'a yadda suke hasashen zabukan za su kasance.

Wadannan dalilai guda uku ne ake hasashen zasu kawowa shugaba Buhari cikas a zaben 2019

1. Rashin adalci wajen nade-naden mukamai

Masu sharhi akan al'amurran siyasa a kasar nan dai na ganin dole ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin duba akan yadd yake yin nade-naden sa saboda al'ummar kudancin kasar na zargin ba yayi masu adalci.

Duk da dai shugaban kasar ya sha karyata hakan.

2. Yiwuwar sasanci a tsakanin 'yan takarar adawa

Haka ma dai ana ganin idan har 'yan adawa musamman ma na jam'iyyar PDP dake neman tikitin yin takarar da Shugaba Buhari a 2019 suka hada kan su suka fitar da mutum daya kwakkwara, to lallai za su iya kayar da shi.

3. Rarrabuwar kuri'un yankin Arewa

Kowa yasan da yawa daga magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari, duk daga yankin arewacin kasar nan suke. To ana ganin idan har jam'iyyun adawa suka raba kawunan 'yan arewar musamman ma wajen kuri'un su, to tabbas za su iya kada shi a zaben.
Naija.ng

Post a Comment

 
Top