Tsohon dan wasan kasar Argentina Diego Maradona ya bayyana cewa ‘yan wasan Super Eagles ta Najeriya sun kusa kasheshi a lokacin da ake buga gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Rasha a watan daya gabata. 

Maradona wanda ya jagoranci kasar Argentina ta lashe gasar a shekara ta 1986 ya bayyana cewa lokacin da Najeriya ta farke kwallonta a wasan karshe na Najeriya da Argentina suka buga na uku a rukuni sai da jininsa yahau. 

Najeriya da kasar Argentina dai sun fito acikin rukuni daya daya hada da kasashen Argentina da Najeriya da Crotia da kuma kasar Iceland sai dai kasar Argentina da Crotia ne suka samu fitowa daga cikin rukunin kuma Crotia har wasan karshe taje a gasar.

 “Lokacin da aka bawa Najeriya bugu fanareti sai dai jini na yahau saboda banyi zaton haka zata kasance ba kuma ‘yan wasan Najeriya sun bani mamaki banyi zaton har yanzu sunada zuciya ba kamar yadda nasansu a baya” in ji Maradona Maradona yana wannan Magana ne a lokacin da ake gabatar dashi a gaban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Dorados ta kasar Medico inda yazama sabon kociyan kungiyar wadda take buga rukuni na biyu a kasar.

“Nayi shekara 14 bani da lafiya saboda yawan shaye shaye da kuma abubuwan da basu kamata ba kuma na dade bana bacci yadda yakamata amma kuma ina fatan a sabuwar kungiya ta zan dawo hayya ci na kuma zan samu nasara da kungiyar” in ji tsohon dan wasan wanda ya taba bugawa Barcelona da Napoli wasa.

👉Me zaka/ki iya cewa ? Rubuta Ra'ayinka/ki ta hanyar comment.

Post a Comment

 
Top