Da yammacin ranar Litinin din nan ne 10 ga watan Satumba 2019, shugaban Majalisar Datijai Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya mika takaradar bukatar neman takararsa shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, ga shugabannin jam’iyyar PDP a hedikwatar jam’iyyar dake Watada Plaza Abuja.
Dakta Saraki ya samu rakiyar manyan ‘yan siyasa daga dukkan bangarorin kasar nan, a takaitattacen jawabinsa, Dakta Saraki ya nemi hadin kan ‘yan jam’iyyar don samun nasarar babbar taron da za a gudanar don fid da dan takarar da zai daga tutar jam’iyyar a zabubkan da za a gudanar a ba gaba, taken yakin neman zabensa ne shi ne #GrowNigeria!
👉Maye Ra'ayinku gameda wannan ?
Yi bayani ta hanyar comments
Post a Comment