Shugaban kungiyar matan gwamnonin Arewa (NGWF) kuma, mai dakin gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar ta shaida cewar kawo yanzu matan gwamnonin Arewa sun himmatu wajen tabbatar da yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma domin tabbatar da samar da al’umma mai cikakken lafiya.
Hadiza ta bayyana hakan ne a jiya a lokacin da take jawabi a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da ta shirya domin ilmantar da wadanda lamarin ya shafa illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman ga mata da matasa.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na Multipurpose da ke Bauchi, ya samu halartar matasa, mata, ‘yan yi wa kasa hidima, sarakuna, limamai, jami’an hukumar hana shan miyagun kwayoyi, ‘yan sanda da sauran wadanda lamarin ya shafa domin tabbatar da rage yawaitar shaye-shaye a tsakanin matasa da mata wadanda hakan ka lalata musu rayuwa.
Matar gwamnan ta shaida cewar daga cikin hanyoyin da suke bi wajen yaki da shaye-shayen kwayoyi a tsakanin al’umma sun hada da kwamitin shawo kan shaye-shaye, tsarin ilmantar da al’ummomi illar shaye-shaye, samar da aiyukan yi ta hanyar cibiyoyin koyar da sana’a ga mata wanda ta shaida cewar tunin wasu jahohin suka fara aiwatar da shirin kawo yanzu.
Taron ilmantarwa kan illar shaye-shayen wanda matar gwamnan ta shirya da hadin guiwar ma’aikatar mata da walwalar yara ta jihar Bauchi an yi ne da nufin kawo karshen shaye-shaye a tsakanin al’umma musamman mata da matasa, wanda masu ruwa da tsaki suka bayyana cewar shan kwayoyi na lalata rayuwar matasa da kashe kasa
Hadiza ta bayyana hakan ne a jiya a lokacin da take jawabi a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da ta shirya domin ilmantar da wadanda lamarin ya shafa illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman ga mata da matasa.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na Multipurpose da ke Bauchi, ya samu halartar matasa, mata, ‘yan yi wa kasa hidima, sarakuna, limamai, jami’an hukumar hana shan miyagun kwayoyi, ‘yan sanda da sauran wadanda lamarin ya shafa domin tabbatar da rage yawaitar shaye-shaye a tsakanin matasa da mata wadanda hakan ka lalata musu rayuwa.
Matar gwamnan ta shaida cewar daga cikin hanyoyin da suke bi wajen yaki da shaye-shayen kwayoyi a tsakanin al’umma sun hada da kwamitin shawo kan shaye-shaye, tsarin ilmantar da al’ummomi illar shaye-shaye, samar da aiyukan yi ta hanyar cibiyoyin koyar da sana’a ga mata wanda ta shaida cewar tunin wasu jahohin suka fara aiwatar da shirin kawo yanzu.
Taron ilmantarwa kan illar shaye-shayen wanda matar gwamnan ta shirya da hadin guiwar ma’aikatar mata da walwalar yara ta jihar Bauchi an yi ne da nufin kawo karshen shaye-shaye a tsakanin al’umma musamman mata da matasa, wanda masu ruwa da tsaki suka bayyana cewar shan kwayoyi na lalata rayuwar matasa da kashe kasa.
Da yake jawabinsa a wajen taron, Kwamadan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a jihar Bauchi, Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana cewar dole ne a hada hanu waje guda domin yaki da shan miyagun kwayoyi, yana mai bayanin cewar shaye-shaye a tsakanin matasa ya yi kamari a halin yanzu, inda ya bayyana cewar dole ne a dauki matakin dakelewa tun kafin lamarin ya fi karfin jama’a.
Daga bisani ya shaida cewar sun himmatu wajen kamewa da kuma hana shan miyagun kwayoyi, yana mai bayyana cewar a wannan shekarar sun samu kame kayyakin shaye-shaye da daman gaske wanda ya bayyana cewar za su ci gaba da zafafa aikinsu domin dakile lamarin.
Daga bisani ya nuna damuwarsa kan yadda basu da kayyakin aiki wadattu musamman mota, inda ya kirayi gwamnan jihar Bauchi da ya samar musu da irin wadannan motocin sindirin domin tabbatar da aiyukansu a kowani lokaci.
Read More at: https://leadershipayau.com/2018/09/06/mata-sun-fi-maza-shaye-shayen-miyagun-kwayoyi-a-wannan-lokacin-inji-ndlea/
Post a Comment