Tsohon Ciyaman din riko na jam'iyyar PDP, kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya ce dole PDP ta tsayar da dan takara mai nagarta, gaskiya da rikon amana muddin tana son kayar da Buhari a zaben 2019.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da ya yi da jaridar Leadership. Ya kuma yi fashin baki kan wasu batutuwa masu alaka da zabe.
Makarfi ya ce ya yanke shawarar shiga takarar shugabancin kasar ne saboda kwarewarsa da irin nasarorin da ya samu a ayyukan da ya yi a baya. Ya bayar da misalin yadda ya ja ragamar mulkin jihar Kaduna inda ya magance matsalar tsaro ya kuma dai-daita tsakanin jama'a mabanbanta addini da kabila a jihar.
Sanata Makarfi kuma ya ce ya banbanta da sauran masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP saboda irin gwagwarmayar da ya yi na tabbatar da cewa jam'iyyar bata ruguje ba lokacin da aka bashi rikon kwarya. Ya ce wasu sun taimaka masa amma a matsayinsa na shugaba shine nauyin ya rataya a kansa.
Naija.ng
Post a Comment