Suna: Laila
Tsara Labari: Yakubu M. Kumo
Kamfani: Nasara Film Production Kano
Shiryawa: Sale Yaro da Yusuf Dan Da Bai San Yau Ba.
Umarni: Ali Gumzak
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Fati Washa, Rabi’u Rikadawa, Fati Shu’uma, Ladidi Tubless, Malam Inuwa, Hadiza Muhammad, Sa’adatu Yusuf. da sauran su.
A farkon fim din an nuna Laila (Fati Washa) a cikin kotu ita da Malam Tanko (Rabi’u Rikadawa) sun tsaya a gaban Alkali (Malam Inuwa) yayin da alkali ke tuhumar Malam Tanko akan karar sa da Laila ta kawo akan cewar yayi mata ciki har ta haihu. Malam Tanko ya nuna sam bai yarda ba sharri akayi masa, yayin da Laila ta tabbatar wa alkali da cewar Malam Tanko ne yayi mata ciki. A wannan lokacin ne alkali ya daga shari’ar zuwa bayan wani lokaci. Lokacin da aka tashi daga zaman kotu sai Laila ta fito rike da dan ta, ta samu waje a cikin kotun ta tsaya ba tare da ta fita ba, a wannan lokacin ne Nasir (Sadik Sani Sadik) ya fito daga cikin kotun sanye da kayan sa na jami’an tsaro, har ya nufi wajen mashin din sa zai hau sai ya hango Laila a tsaye, bayan ya tambayeta dalilin zaman ta a wajen ne sai ta nuna masa cewar ita ba ‘yar garin bace kuma guzirinta ya kare bata da kudin komawa gida, hakan yasa Nasir ya dauke ta ya tafi da ita gidan sa da nufin washe gari zata koma garin su. Bayan Laila tazo gidan Nasir ne sai ta fahimci bashi da mata ko iyali, washe gari kuwa lokacin da zai fita aiki sai ya bata kudin motar zuwa garin su, bayan ya fita sai Laila ta kwaso kayan sawar sa ta wanke ta shanye, a sanda tazo kwashe kayan akan igiya sai Nasir ya dawo gidan, ganin bata tafi ba sai ya fusata ya nuna mata fushin sa, kuma ya saka ta a gaba har sai da suka bar masa gidan sa ita da dan ta. Har Nasir ya rufe gidan sa sai kuma tausayin ta ya kama shi, hakan ne yasa yaje ya kira ta ya dawo da ita gidan sa sannan ya bukaci ta bashi labarin abinda ya faru da ita wanda har ya zamo sanadin da ta haifi dan da bashi da Uba. Akan Laila ta fara bashi labarin cewar ta taso ne a wajen mahaifiyar ta wata mai abinci da suke zaman kan su. Kuma a wajen ta hadu da Alhaji Tanko (Rabi’u Rikadawa) wanda yake zuwa siyan abinci wajen mahaifiyar ta. 

Kuma ganin ta da yake yi ne ya soma kulata yana kashe mata kudi, akwai lokacin ma da ya dauke ta ya kaita wajen da zatayi cefanen kayan abinci, a sannan ne ya bata kudi masu yawa wanda hakan yaja ra’ayin ta har suka tsara cewar zasu yi tafiya don suje wani garin su huta, tun daga sannan suka fara mu’amula wanda har daga baya Laila ta samu juna biyu, kuma tayi kokarin ganin ta zubar da juna biyun amma da taje asibiti sai aka tabbatar mata da cewar idan ta zubar da juna biyun zata iya rasa rayuwar ta. Hakan ne yasa ta fasa zubar da juna biyun kuma ta sanarwa da Alhaji Tanko tana dauke da juna biyu amma sai ya nuna sam ba nashi bane, ganin haka ne mahaifiyar Laila (Ladidi Tubeless) ta kira Alhaji Tanko gami da nuna masa cewar juna biyun dake jikin Laila nashi ne saboda dashi kadai take mu’ula, amma sai Alhaji Tanko ya nuna wa mahaifiyar Laila cewar kada a sake danganta juna biyun Laila da dan sa idan ba haka ba zai jefa su a cikin masifa, jin hakan ne yasa Laila taje har ofis din Alhaji Tanko ta fada masa cewar dole ya karbi juna biyun jikin ta a matsayin dan sa idan ba haka ba kuma da zarar ta haihu zata mika sa a kotu. Hakan kuwa akayi bayan Laila ta haihu sai ta shigar da kara kotu amma duk da haka Alhaji Tanko bai karbi yaron a matsayin dan sa ba. Lokacin da Laila ta gama bawa Nasir labarin abinda ya faru da ita sai tausayin ta ya kama shi kuma yaji yana sha’awar auren ta saboda ya samu damar yin jihadi ta hanyar auren ta don ta daina harkar karuwancin da ta jefa kanta. 

Bayan an sake zama a kotu Alhaji Tanko dai bai amsa cewar dan da Laila ta haifa nasa ne ba. Lokacin da aka fito daga kotu sai Nasir ta kira Alhaji Tanko suka tattauna akan yana so Alhaji Tanko ya fadawa Alkali gaskiyar cewar dan da Laila ta haifa nasa ne, idan yayi haka shi kuma Nasir yayi alkawarin zai auri Laila kuma zai karbi yaron a matsayin dan sa. Jin hakan sai Alhaji Tanko ya amince, Laila ma ta amince da cewar zata auri Nasir, haka suka je ofis din alkali aka yi sulhu, Alhaji Tanko ya amsa cewar dan da Laila ta haifa dan shi ne. Daga bisani aka daurawa Laila da Nasir aure ta tare a gidan sa. 

Laila sun fara zama cikin aminci ita da Nasir har zuwa lokacin da ta sake haifar ‘ya mace. Bayan wasu ‘yan shekaru sai Laila ta sacewa Nasir kudin da yake tarawa kuma yake ajiyewa a gida, Laila ta sace kudin fiye da miliyan daya, sannan ta dauki ‘yar ta mace ta gudu da it’s ta bar da namijin a gidan Nasir kuma ta rubuta masa wasikar cewa ta gama zama dashi dama abin hannun sa take so yanzu kuma tunda ta samu zata tafi inda ba zai kara ganin ta ba kuma zata fara sana’ar siyar da abinci a can. Jin hakan ne ya tashi hankalin Nasir yaje wajen mahaifiyar ta mai siyar da abinci ya fada mata Laila ta gudu, amma sai ta nuna masa cewar ita batasan inda Laila ta tafi ba kuma kada ma yace zai kaita kotu domin ba itace asalin mahaifiyar Laila ba, daga kauye ta dauko ta a wajen wata kawar ta wadda ita ma ‘yar duniya ce.

 Anan dai mai abincin ta kwatantawa Nasir gidan da ta dauko Laila a kauye. Bayan take gidan sai ya tarar ashe mahaifiyar Laila makauniya ce kuma Laila tana da kanwa (Fati Shu’uma) wadda itama yawon bariki take yi a cikin kauyen. Lokacin da Nasir yaje kauyen ya sanarwa da ainahin mahaifiyar Laila (Hadiza Muhammad) cewar Laila ta gudu, sai suka sanar masa da cewar Laila ta kira wayar su tace zata zo kauyen ta dauke su gaba daya su koma Kaduna da zama. Kwatsam su Nasir suna zaune gaba daya sai wani mutumi ya shigo gidan ya sanar musu da cewar su Laila sun yi hatsari mota ta fadi dasu kuma Laila ta mutu amma ‘yar ta tana raye. Bayan an kawo gawar Laila sai Nasir ya dauki ‘yar sa duk da mahaifiyar Laila taso ya bar mata ‘yar amma sai ya nuna shi ba zai bar ‘yar sa a gidan da babu tarbiyya ba. Haka ya soma birni amma sai kanwar Laila ta biyo shi gida akan tana so ya aure ta. Amma sai Nasir ya nuna ba zai iya sake auren mutane irin ta marasa tarbiyya ba. Bayan dan wani lokaci Nasir yayi sabon aure ya auri wadda yake ganin zata rike masa ‘ya’yan sa da amana.

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya fadakar, kuma ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba.
2- Sauti ya fita radau, camera ma ba laifi.

Kurakurai:

1- Lokacin da Laila ta fito daga cikin kotu kuma ta sanar da Nasir cewar guzirin ta ne ya kare shiyasa ba zata iya tafiya garin su a wannan lokacin ba. Tunda an nuna cewar ba dare ne yayi ba, ya dace Nasir ya bata taimakon kudin motar komawa garin su ba sai tazo gidan shi ta kwana ba. Idan kuma ana son nuna wani sako a gidan sa ne, to ya dace yace bashi da kudi amma idan ta kwana a gidan sa washe gari zai samu kudin da zai bata.

2- Shin wai kotun da Laila ta kai kara babu lauyoyi ne? Har aka gama shari’ar me kallo bai ga lauya ko a wajen zaman sa ba.

3- Tun da aka fara shari’a har aka gama ba’aga marikiyar Laila a kotun ba (Ladidi Tubeless) ya dace a nuna marikiyar Laila a wajen tunda an nuna tana goyon bayan abinda duk Laila take aikatawa.

4- Bayan wasu shekaru da yin auren Laila da Nasir me kallo yaga cewar Nasir ya tashi daga gidan sa ya koma sabon gidan da yafi nasa kyau, amma bayan Laila ta gudu daga gidan Nasir sai aka ga Nasir da marikiyar Laila a tsohon gidan sa da ya bari suna tattauna matsalar guduwar da Laila tayi, tunda an nuna wa me kallo cewar Nasir ya sauya gida to bai dace daga baya a gan shi a tsohon gidan sa ba, a hoto na gaba kuma sai aka ganshi a sabon gidan sa, ya dace a nuna wa me kallo dalilin yin hakan.

Karkarewa:

Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, amma tun a farko-farkon fim din an riga an samar da masalahar da bai dace a kara jan mai kallo ba, yin hakan zai iya jawo matsalar da fim din zai gundiri me kallo, domin ya riga yaga warwarar matsalar da aka fara tufkawa. Wallahu a’alamu.

Read More: https://ift.tt/2wQT273

Post a Comment

 
Top