Munji cewa, Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana'a ya fito ta shafin shi na yanar gizo inda ya godewa Allah da yayo shi baki duk da cewa mahaifiyarshi farace.



Musa ya kara da cewa, auren farar mace ba shine zai tabbatar da cewa zata haifi fararen 'ya'ya ba inda a karshe ya soki masu bilicin.

Ashe dai wannan magana da yayi yana mayar da martanine akan wani barkwanci da akayi a kanshi, inda wata baiwar Allah ta rubuta a shafinta na dandalin Twitter cewa, Yin bleaching ba shine matsalar ba, sai kana tunanin zata haifa maka Ibrahim Maishinku, kwatsam sai ga Musa Mai Sana'a.

Wannan lamari ya dauki hankulan mutane inda aka yi Raha.

Amma shi Mai Sana'a batamai dadi ba, shiyasa ya tunzura yayi wancan rubutu.


Dan jin Ra'ayinku kuyi comments

Post a Comment

 
Top