Dakta Michael Oguntoye likita ne da ya kware a bangaren kiwon lafiya da kuma yadda kwayoyin cututtuka ke yawo tsakanin mutum da saura abubuwan da mutum ke mu’amala da su a matsugununsa.


Likita Oguntoye ya yi gargadi ga al’umma kan tasirin da wayar hannu ke da shi wajen yada kwayoyoyin cuta da suka hada da kwayar cutar ‘Virus’ da dai sauransu.

Likita ya ce, wayoyin hannu kan yi yawo tsakanin mutane a kowace rana bisa dalilai da dama da suka hada da nuna wani hoto ko bidiyo ga aboki ko wani wanda aka hadu akan hanya.

Wani lokaci ana kai waya wajen mai caji kuma a wannan lokaci waya na sauya hannaye daga mai ita zuwa wanda ya aika, in aikawa ya yi, zuwa mai cajin wayar da dai sauran yadda wayoyi ke da ikon sauya hannaye a kowace rana.

Wannan yawo da wayar hannu ke yi na bata damar shuga wasu hannaye na wasu masu dauke da cututtuka ko kuma wadanda suka taba wani abu mai dauke dakwayoyin cututtuka. Kuma da zarar an taba wayar da irin wannan hannu, to babu shakka za a bar wasudaga cikin kwayoyin cutar a jikin wayar, kuma wannan zai bayu ga yawon kwayoyin cutar ga duk wanda ya kara taba wayar.

Likita ya shaidawa kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya cewa, matasa na yawan shiga da wayoyin hannunsu cikin bandaki a yayin da suka shiga wanka ko uzurin biyan bukatarsu. A nan ne wayoyi ke nadar kwayoyin cututtuka kamar su ‘Virus’ da ‘Bacteria’.

Likitan ya ja hankalin al’umma da su kaucewa shiga da wayoyinsu cikin makewayi da kuma kiyaye kiwon lafiya a duk lokacin da wayoyinsu suka sauya hannaye ta hanyar yin amfani da ruwan magani mai kashe kwayoyin cuta da a ke kira da disinfectants.

Read more at: https://ift.tt/2wMX8h0

Post a Comment

 
Top