Jaridar The Guardian, ta bankado wasu muhimman alfanu da sirri da ke tattare a cikin ganyen Mangwaro wadanda ke da matukar amfani ga lafiyar dan Adam.
A yayin da binciken masana kiwon lafiya ke ci gaba da bunkasa da kuma kara fadi ta fuskar zamani na kimiyya, ya tabbatar da cewa mafi akasarin magunguna da aka samar da su daga tsatso na itatu sun fi tasiri ga lafiya da kawar da cututtuka a jikin dan Adam akan kowane nau’in magani.
Binciken da kwararru na bangaren kiwon lafiya suka gudanar ya tabbatar da cewa, baya ga amfani na ‘ya’yan itaciyar Mangwaro akwai kuma tarin arziki da ganyen itaciyar ya kunsa.
Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani wanda suka hada da; tannins, anthocyanidins, beta-taraxerol, ethyl acetate da sauransu.
A sakamakon wannan arziki na sunadarai da ganyen mangwaro ya kunsa da kuma tasiran su ga lafiyar dan Adam, mujallar Alummata ta kawo maku jerin wasu cututtuka da idan anyi amfani da Ganyen na Mangwaro akan samu waraka da izinin Mabuwayi.
1. Domin Ciwon Suga- Ana amfani da busasshen ganyen mangwaro da aka nike shi ya zama gari wajen magance cutar suga tun a matakinta na farko sakamakon tasirin sunadaran anthcyanidins da kuma beta-taraxerol da ya kunsa. Kazalika ana kuma jika ganyen magwaro cikin ruwa na kwana guda kana a kwankwadi wannan ruwa domin magance cutar ta suga tun kafin ta ci karfin lafiyar dan Adam.
2. Cutar Hawan Jini- Ganyen Mangwaro ya na da matukar tasiri wajen saukaka cutar hawan jini ta hanyar inganta kuzari na tashoshi da shiyoyi masu aika sakonni na jini.
3. Kasala da rashin karfin jiki- Akan dumama ruwan wanka tare da ganyen mangwaro domin aikata hakan yana kawar da kasala tare da kara kuzari ga dan Adam.
4. Tsakuwar ‘Koda- Ana amfani da gari na ganyen mangwaro wajen kawar ta wannan cuta sakamakon narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.
5. Cututtukan tashoshin numfashi- Ana amfani da markadadde ganyen mangwaro tare da ruwan Zuma yana kawar da duk wata cuta da ta shafi tashoshin numfashi irin su Mura, Tari, Asma, disashewar murya da sauransu.
6. Cutar Atini- Akan kwankwadi Garin Ganye Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.
7. Ciwon Kunne- Akan dumama ruwan da aka tatso daga jikin Ganyen Mangwaro wajen digawa a cikin kunne domin kawar da radadi da cututtuka da suka shafi cikin kunnen dan Adam.
8. Waraka ga ‘Konuwa- Bincike ya tabbatar da cewa ana ‘kone ganyen mangwaro kana a yaryada tokar sa domin waraka ga ‘konuwa akan fatar dan Adam.
9. Cutar maƙoshi da shaƙuwa- Hayaki daga jikin konannen ganyen mangwaro yana kawar da cututtukan da suka shafi Maƙoshi/Maƙogoro da kuma cutar shaƙuwa.
10. Ciwon ciki- Ko shakka ba bu ana jika ganyen mangwaro a kwana kana a kwankwadi ruwan da sanyin safiya kafin a jefa komai a baka domin hakan yana kawar da cututtuka da dama da suka shafi cikin bil Adama.

Read more at: https://ift.tt/2wMX8h0
Post a Comment