Daga Dauda Umar Januhu

Rahoton daga garin Badarawa dake karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara sun tabbatar da mutuwar kimanin mutane 11 tareda raunata kimanin 23.

Maharan dai sun shigo garin ne na Badarawa da misalin karfe 9:30pm na dare inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wakilinmu ya samu tattauwa da wani mazauni garin inda yake bayyana cewa yanzu haka an kai wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka zuwa asibitocin garin Shinkafi da kuma Gusau babban birnin jihar.




Post a Comment

 
Top