An zargi wasu jami'an yansanda da haddasa wani hadarin mota a garin Nkalagu a jihar Enugu.ranar Lahadi. Rahotanni sun ce jami'an yansandan sun biyo wata mota ce a guje bayan direba ya ki tsayawa lokacin da suka tsayar da shi domin gudanar da aiki, amma garin gudu sai burkin motar ta kasa, sakamakon haka motar ta kwace ta nufi wasu motoci da ke tafe kuma ta yi karo da su.
Wannan lamari ya sa jama'a da dama sun sami munanan raunuka kamar yadda ganau ba jiyau ba Mazi Ogbonna ya shaida wa manema labarai.
Hakazalika rahotanni sun yi zargin cewa jami'an yansandan sun tsere daga wajen bayan wannan hadarin ya faru.
Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
Post a Comment