'Yan takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC ne INEC ta bayyana cewar sun yi nasara a zaben maye gurbi da aka yi a jihohin Bauchi, Katsina, da Kwara. A jihar Katsina, Abubakar Kusada na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben maye na mazabar Kankia/Kusada/Ingawa. Kusada ya samu kuri'u 48,518, fiye da na dan takarar da ke biye ma sa, Abdulssamad Yusuf na jam'iyyar PDP.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Rasheed Adebayo, baturen hukumar zabe, ya sanar da cewar Kusada ne ya lashe zaben bayan samun kuri'u ma fi rinjaye. Yusuf Nuhu, dan takarar jam'iyyar APC, ne ya lashe zaben maye gurbin kujerar dan majalisar wakilai na mazabar Toro a jihar Bauchi. Dan takarar na APC, Yusuf Nuhu, ya samu kuri'u 22,317 yayin da Shehu Buba na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 18,235. Nuhu ya samu nasara a mazabu 11, yayin da Buba ya lashe mazabu 3 kacal.

Legit hausa

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Ahmad Tijjani Fagam, ya ce dan takarar jam'iyyar APC ne ya lashe zaben saboda ya samu kuri'u ma fi rinjaye. A daren jiya, Asabar, ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaben maye gurbi na kujerar majalisar wakilai ta mazabar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abimbola Adesoji, baturen zabe na hukumar INEC, ya bayyana cewar APC ta samu kuri'u 21,236 yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 18,095. Ya kara da cewar Labour party ta samu kuri'u 150, jam'iyyar PPN ta samu kuri'u 76, sai kuma jam'iyyar UPN da ta samu kuri'u 42. Farfesa Adesoji ya ce an kada jimillar kuri'u 40,930 a zaben, adadin kuri'u 1,331 ne su ka lalace.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top