Fitaccen dan wasan Hausa Muhammadu Sani Idris Kauru wanda aka fi sani da Moda ya ce an kitsa labarin mutuwarsa da zummar cutar da shi.
A tattaunawar da BBC ta yi da shi a cikin jerin shirye-shiryeta na magance matsalar labaran karya, Moda ya ce bai ji dadi ba lokacin da aka rika yada labaran da ke cewa Allah Ya yi masa rasuwa.
A watan Mayu ne dan wasan na Hausa ya sha fama da rashin lafiyar da ta kai ga kwantar da shi a asibiti. Daga bisani ne aka rika yada jita-jitar cewa ya riga mu gidan gaskiya.
Sai dai hakan ya sa wasu abokan sana’arsa suka ziyarci asibitin suka dauki hotunan da aka watsa domin karyarta labarin mutuwarsa.
Shahararren dan wasan ya shaida wa BBC cewa hankalinsa ya tashi lokacin da ya samu labarin da ake watsawa na mutuwarsa.
“Hakika a wancan lokacin hankalina ya tashi saboda ban yi wata rashin lafiya da na gigice ba, wadda za a ce sakamakon hakan na fita hayyacina ba,” in ji shi.
Moda ya kara da cewa ransa ya yi matukar baci saboda an tashi hankulan iyalai da masoyansa, yana mai cewa wadanda suka baza labarin sun yi ne “domin su cutar da irinmu da muka yi fice.”
Sources:aminiyahausa.com

Post a Comment