Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Muhammad ta bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar basu raba kawunan jaruman masana'antar Kannywood ba.

Fati ta bayyana hakane a wata hira da tayi da jaridar Daily Trust inda ta bayyana cewa, suna yin 'yancinsu ne da kundin tsarin mulki ya baiwa ko wane dan kasa na zabar dan takarar da yake so kuma abune na ra'ayi, kowane jarumi yakan bi mutumin da yake tunin shine zai fi kawowa Najeriya ci gaba kuma suna yi ne dan ci gaban kasa.

Fati ta kara da cewa, bayan zabe Kannywood zata ci gaba da wanzuwa dan haka basu bari siyasa ta shiga tsakaninsu ba.

Da aka tambayeta kan cewa ta bar harkar fim zuwa siyasa, Fati tace a yanzu itace shugabar gudanarwa ta kamfe din Jam'iyyar PDP a yankin Arewa Maso Yamma dan haka tana tsundum cikin siyasa kuma tana kokarin jawo ra'ayin jarumai 'yan uwanta wanda zasu yi wannan tafiya tare.

Fati tace wannan karin masana'antar Kannywood ta samu ci gaba sosai lura da irin yanda aka daukesu da muhimmanci a siyasar kasarnan ta yanda aka sakasu cikin wanda zasu iya kawo canji kan yanda ake gudanar da harkokin kasar ba kamar a bayaba ta yanda saidai kawai lokacin zabe da kuma an gama shikenan a yaddasu.

Fati ta tabbatarwa da Masoyanta cewa tana nan tare dasu a koda yaushe.

Post a Comment

 
Top