Wallahi daga yau na daina sauraron fatawar Aminu Ibrahim Daurawa, don kuwa babu abin da ke cikinta sai tsabar son zuciya, da marawa jinsi guda baya, ko da kuwa, ba su da gaskiya. 
Haka kawai Malami ya zama na bangare guda? A ma'auninsa duk abin da mace ta yi wa mijinta na rashin kyautawa, zaluntarta aka yi - ko kuma duk fushin da za ta yi a kan ko mene ne, rarrashinta za a yi. Amma shi namiji, ba shi da wata mafaka a wajensa, duk abin da ya yi wa matarsa rashin kyautawa ne da rashin adalci? 

Haka, ake malanta? Duk ya janyo, matanmu sun raina mu, suna ganin kawai cutarsu muke yi? Kuma wallahi, idan ma yana yi ne don ya burge su, babu macen da zai burge, don kuwa abubuwan da yake fada a yi musu, ko shi bai isa ya yi musu ba. Aikin banza! 

Yadda kuka ga rubutun nan a fusace, haka na tsinkayo muryar wani magidanci a fusace na furta wadancan kalmomi da ma wadanda suka fi su zafi kan Malam Aminu Ibrahim Daurawa, a tsakiyar kasuwar Sabon Gari. 

Da dai na so na kai gare shi, don jin, me ya yi zafi haka, da ido zai ci wuta? Sai kuma na lura a sama yake kololuwa - kar na je ni ma na samu rabona. Don haka na garzayo gare ku, ma'abota sauraron shirye-shiryen fatawoyin da Malam Aminu Ibrahim Daurawan ke yi:

WAI SHIN IKIRARIN DA WANCAN MUTUM KE YI GASKIYA NE? KO KUWA SHIFCIN GIZO NE?

Daga:Maje  El-hajeej Hotoro

Post a Comment

 
Top