Shima dai mawaki aminu alan waka ya tofa albarkacin bakinsa kan wannan harka ta samun cigaban masana'antar su.
Ga bayyaninsa kamar haka:-
"KANNYWOOD INDUSTRY Ta sami wakilcin kirki da nagarta a wajen gabatar da kudurorinta na bunkasa Masana'antun Guda biyu. Ba wannan karon bane kadai aka fara samun damar shiga Fadar shugaban kasa, sai dai a wannan karon ne aka shiga da niyyar mika koke da bukatun Kannywood kuma cikin Sa'a Shugaban kasa ya karba. Saboda rungumar abin hannu biyu, har aka nada wakilai cikin lokaci suka sake zama na musamman da shugaban Ma'aikata na kasa Abba kyari aka tsaida mafita akan kyakkyawan Hadafi. Muna jaddada godiyarmu ga mai girma shugaban kasa Allah ya kara lfy ya idda muradi. Muna sake mika godiya ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo Musamman a gabar da ya dauki Alkawarin Bunkasa wakar da muka yi ta zaman lfy Al-umar Nijeriya. Ban gusheba da gaisuwata ga Dr. Aisha Buhari musamman yarda ta karrama mu da Nuna kaunarmu da Sana'armu. Mutane irin Alh. Nasir Dano Dan Amanar Dutse babu kalmar da ta dace ta yabon abinda suka yi mana face addu'a. Na hada da Agogo Sarkin Aiki sakataren Gwamnati Mustafa Boss, Zan Rufe da Dujiman Adamawa Alh. Musa Halilu, wanda ya dauki gabarin tafiya da mu kan jiki kan karfi har illah ma sha Allahu. Da yawun mawaka yan uwana muna jaddada godiyar wannan karamci Allah ya cika mana kudurinmu na sake maimaita kujera a shekara ta 2019".
Post a Comment