Durfa shine Ciyaman din kwamitin direktoci na Kwallejin Fasahar Kiwon Lafiya da ke Zawan a jihar Plateau

- Shine ma'aikacin gwamnati na biyu da ya yi murabus sakamakon zargin almundaha da ya ke ganin gwamnatin jihar tayi a zabukkan kananan hukumomi

Ciyaman din direktocin Kwallejin Fasahar Kiwon Lafiya da ke Zawan a jihar Plateau, Nandul Durfa, ya yi murabus daga kujerarsa a kan dalilin magudin zabe da almundaha da ya yi ikirarin an tafka a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar a ranar 10 ga watan Oktoba.



A wasikar murabus din da ya aike wa sakataren gwamnatin jihar, Durfa ya bayyana cewa ya yi murabus din ne saboda ya samu kwanciyar hankali domin zuciyarsa ba za ta iya samun natsuwa ba bisa barnar da gwamnatin jihar ke aikatawa.


Durfan, wanda jigo ne a jam'iyyar APC kuma tsohon shugaban Asibitin Kwararu da ke Gwagwalada a Abuja ya ce a lokacin da aka gudanar da zabe a Sabon-Gida da ke karamar hukumar Langtang ta Kudu, gwamnati ta hana wanda ya lashe zaben inda ta nada wanda ya sha kaye.

"Ina da tabbas cewa jami'in zaben bai karbi sakamakon zaben daga akwatunnan zabe ba kwatsam ya tafi Jos inda ya bayyana sakamakon zabe, kuma na samu rahoton cewa hakan aka yi a sauran gundumomi.
"Irin wannan zaluncin zai iya janyo rashin amincin tsakanin gwamnati kuma daga baya ya janyo rikici, inji shi.

Ya kara da cewa a matsayinsa na kirista wanda ya ke kokarin ganin ya aikata ayyukan da za su kai shi ga shiga aljanna ya zama dole ya yi murabus daga irin wannan gwamnatin.

Sources:legit.ng/hausa

Post a Comment

 
Top