Kimanin mata 50 ne suka yi yunkurin kashe wata mata ta hanyar duka a garin Aba na jihar Abia  bayan sun zarge ta da kasancewa cikin wadanda suka yi awon gaba da kudinsu kusan fiye da N50m a wani tsarin adashen damfara na Unique Women.

Rariya.ng ta ganao cewa Unique Women tana karbar N40.000 ne daga kowace mace, da sunan kasuwanci, daga bisani kuma ta bayar da N70.000 bayan kowane kwanan 7.

Bayanai sun ce bayan wasu kwanaki sai aka kula an rufe ofishin Unique Women da kwado, sakamakon haka zargi ya shiga. Wata majiya ta ce an rutsa da wata mata da ke cikin jami'an Unique Women a wani Banki a garin Aba, inda mata suka yi kokarin halakata, amma 'yansanda suka cece ta kuma suka tafi da ita caji ofis.

Yanzu haka matara tana hannun yansanda a jihar Abia inda take fuskantar bincike tare da wasu mutane da ake zargin suna gudanar da wannan harkar tare.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us. 

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top