Yunkurin Tozarta Dan takarar Shugabancin kasar nan Atiku Abubakar a Filin jirgin sama ya samu tasgaro ta yadda a ka yi amfani da jami'an tsaro wajen yunkurin Sanya masa Kudaden Kasashen Ketare domin cimma wata manufa ta daban.

Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC Kwamared Timi Frank, shi ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce an yi kokarin Bata Sunan Dan takarar Shugabancin Kasar nan a lokacin da ya sauka Najeriya daga Kasar Dubai. 

Frank ya cigaba da cewa Atiku, wanda ya dawo yau Lahadi da Misalin karfe 1 na Rana daga Hutun da ya tafi a can kasar ta Dubai saukar sa ke da Wuya sai muka ga jami'ai na Musamman sun sauka suna Binkicen jirgin da Atiku ya fito  tare da daukar faya-fayen Bidyo da Hotuna a cikin jirgin da wajen sa.

Bayan sun gama duk binkicen su na tsawon lokaci basu ga komai a jikin Atiku Ko cikin jirgin sa ba duk da sun yi kokarin ajiye wata jaka makare da kudaden kasashen waje gami da wasu kaya na laifi amma dai Shirin nasu ya samu cikas Inji shi. 

Ya kara da cewa dama dai sun shirya shirin ne Idan Atiku Ya sauka Najeriya sai a nu na ma duniya cewa ya zo da wasu kudade da kuma wasu kayan laifi duk da mun san Yanzu haka Fadar Shugaban Kasa tana Cikin Alhinin rashin yin nasara a wannan shiri na Bata Atiku da ta kwashe lokaci tana kitsawa.

Frank ya ce don haka muna Allah wadai da wannan yunkuri na fadar Shugaban Kasa karkashin Jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari tare da yi masa tuni da cewa da tsohon shugaban kasa Ebele Johnathan ya yi masa irin wannan a zaben 2015 ai da bai zama shugaba ba a yau. 

Kazalika ya ce tun lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Ya yi Mulki Shekaru Takwas yau ne na farko da a ka fara caje jikin sa a filin sauka da tashin jiragen Sama a duk duniya. 

Ya kuma ce muna gargadi ga fadar shugaban kasa da cewa ta kama Mutuncinta kuma ta guji yin duk wani Shiri na Bata Sunan dan takarar jam'iyyar PDP.

Domin muna da wani labari daga majiya mai tushe na irin kulle-kullen da kuke yi game da Dan takararmu don haka muke kira da Babbar Murya ga Hukumar Sanya Idanu ta kasa da Kasa da su duba wannan Al'amari da idon basira na yadda a ke Tsorata dan tarakar adawa wanda ya yi Mataimakin Shugaban Kasa tsawon Shekaru 8.

Sa Hannu:
Kwamared Timi Frank
Tsohon Mataimakin Sakataren yada labarai na APC.

Jaridar Dimokuradiyya 11/11/2018.

Post a Comment

 
Top