Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana cewa kociyan kungiyar na yanzu na rikon kwarya Santiago Solari zai ci gaba da zama a matsayin kociyan kungiyar a karshen kakar nan da a ke bugawa kamar yadda rahotanni suka bayyana. 

Solari dai yasamu goyon bayan ‘yan wasan kungiyar tare da wasu daga cikin shugabannin kungiyar bayan yasamu nasara a wasanni uku daya jagoranci kungiyar a jere da suka hada da wasan daya buga da kungiyar Manilla a gasar Copa Del Rey da kuma wasa da Baladolid na gasar Laliga sai kuma wasan zakarun turai da suka samu nasara daci 5-0 akan kungiyar Biktoria Plzen. 

Sai dai wasu masana wasanni suna ganin daman can Real Madrid zata iya buga wasa kuma tasamu nasara akan wadannan kungiyoyin da Solari yasamu nasara akansu saboda haka sai ya buga wasu daga cikin wasannin da ake ganin manyan ne sannan za’a amince da kokarinsa. Sai dai shugaban gudanarwar kungiyar, Florentino Perez, zaici gaba da neman mai koyarwa  babba wanda zai karbi kungiyar anan gaba inda aka bayyana cewa kungiyar tafi son Mauricio Pochettino na kungiyar Tottenham. Sai tsohon kociyan Chelsea, Antonio Conte da kociyan tawagar ‘yan wasan Belgium, Roberto Martinez, wanda dan kasar Sipaniya ne yayinda shima kociyan Manchester United Jose Mourinho yake kan lissafinsu.

 Solari dai ya buga wasanni a Real Madrid na tsawon shekaru biyar kuma kafin yazama kociyan kungiyar na rikon kwarya shine mai koyar da matasan ‘yan wasan kungiyar da ake kira Real Madrid Castilla.   


Post a Comment

 
Top